KARANCIN ABINCI: CBN ta bada daman a shigo da Tan 262,000 na Masara Najeriya

0

Babban Bankin Najeriya ya ba da izinin a shigo da tan 262,000 na masara domin rage radadin tsananin karancin abinci da ya addabi mutanen Najeriya.

” A dalilin tsananin rashin abinci da ya dabaibaye ‘yan Najeriya, Bankin CBN ya ba wasu kamfanoni daman su shigo da masara kasar nan.

Kamfanonin sun hada da:

1 – Wacot and Chi Farms Limited

2 – Crown Flour Mills

3 – Premier Feed Mills Company Limited

Wadannan kamfanoni za su shigo da masaran ne a cikin watannin Agusta, Satumba da Oktoba.

Sanarwar ya kara da cewa in bada wadannan Kamfanoni da aka zayyano ba aamince wa ko wa ya shigo da kayan abincin ba.

Hukumar hana fasakwauri ta kasa, ce ta fitar da wannan sanarwa ta hannun mataimakin Kwanturola Janar, T.M Isa.

Share.

game da Author