Kamfanin BUA, ɗaya daga cikin mashahuran kamfanonin da ke sahun gaba a Afrika wajen sarrafa abinci, ma’adinai da sauran ayyuka, ya sa hannu a yarjejeniyar kafa matatar ɗanyen man fetur, wadda za ta riƙa tace tan milyan 10 a duk shekara.
Ya kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin ƙasar Faransa mai suna Axens na France domin kafa matatar a jihar Akwa Ibom tare kuma da kafa sashen sarrafa sauran sinadaran danyen mai.
Matatar wadda za ta ci bilyoyin daloli ba ma nairori ba, za ta rika samar da mai samfurin Euro-V ga kasashen Afrika ta Yamma da cikin Najeriya
Kamfanin BUA, mallakin Abdulsamad Rabi’u, ya ce ya yi hadin-guiwa ne da kamfanin na Faransa saboda cancantar sa.
Wannan gagarimar yarjejeniya dai Shugaban BUA shi da kansa, Abdul Samad Rabiu da Shugaban Axens, Jean Sentenic suka sa mata hannu a wani gagarimin taron da tawagar Ministan Cinikayya da tattalin arziki suka jagoranta.
Abdul Samad Rabiu ya ce, “masana’antar za ta rika ta ce tan milyan 10 a duk shekara na fetur da sauran sinadaran mai daban-daban. Kuma akasari duk da kayan cikin gida za a yi amfani.
“Ya zame wa kamfanin BUA jini da jijiya ya ga cewa ya kirkiro da kuma kawo canji da cigaban harkokin kasuwanci. Ku dubi masana’antar simintin mu. Ku dubi masana’antar sukarin mu.” Inji Abdul Samad.
Shi ma Shugaban Kamfanin Axens, Jean Sentenic ya ce: “Mu na farin ciki da alfaharin kasancewar mu cikin wadanda za su kawo wannan gagarimin ci gaba na zamani a kasuwancin harkokin sinadaran mai ingantacce.
“Wannan kasaitacciyar masana’anta za ta sa BUA ya rika samar da sinadaran tataccen mai kala daban-daban a cikin kasar nan kuma mai inganci.”