KAKA-TSARA-KAKA: Yadda Amurka ke bibiyar hada-hadar kudaden Atiku da matan sa a bankunan kasashen duniya

0

Kafin zaɓen 2019, Atiku ya fito gadan-gadan ya riƙa fuskantar duk wani zargi da yarfen siyasa, domin ya nuna wa duniya cewa ba shi da wani kashi a gindi da har za a rika kyamatar kasancewar sa shugaban kasa, idan har ya ci zabe.

“Na sha fada wa masu yi min yarfe cewa idan su na da shaidar cewa na wawuri kudade, to su kawo shaida. Amma babu wanda ya iya kawo wata shaidar komai har yau.”

Haka Atiku ya bayyana da babbar murya, lokacin kamfen a garin Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.

A lokacin da Atiku ke ta wannan bambami da cika baki, ashe gwamnai Amurka na can na kulafuci, bimbini da bin-diddigin harkokin da Atiku ke yi, har da bankunan da ya ke ajiya da tasarifin kasuwanci, domin su samu wata shaidar da za a iya amfani da ita.

Nan da nan Sashen Binciken Harkallar Kudade na Babban Bankin Amurka (FinCEN) ya dukufa bin-diddigin harkokin kudaden Ariku da dukkan iyalan sa sau-da-kafa.

Bincike ya nuna FinCEN sun gano wasu wasu shige-da-ficen kudade da aka yi, wadanda su ke zargin cewa akwai lauje a cikin nadi.

Wannan bincike da su yi, ya fito da zargin cewa akwai yiwuwar an rika karkatar da wasu makudan kudade a kasashen duniya da sunan Atiku, ta hanyar yin amfani da kamfanin hada-hadar danyen mai, Shell.

FinCEN tare da wani gungun Kwararrun ‘Yan Jaridar Binciken Kwakwaf na Duniya su 108, ciki har da PREMIUM TIMES, sun tattara wasu shimin dimbin takardun bayanan rahotannin sakala-sakalar kudade da shugabannin duniya su ka yi.

Akwai kuma harkallolin da ‘yan ta’adda da manyan dillalan muggan kwayoyi su ka yi da kuma rikakkun masu karkatar da kudade daga wannan kasa zuwa waccan.

BInciken wadannan shugabanni da sauran harkalla ya dauki kwararrun ‘yan jarida 400 tsawon watanni 16 su na bincike a cikin kasashe 88. Cikin su kuwa har da wasu ‘yan PREMIUM TIMES.

Dammam fayil-fayil da su ka shigo hannun wadannan garken ‘yan jarida sun hada har da wadanda bankuna su ka bayar da su ke zargin cewa kudaden harkalla ne wato (SARs), ko kuma ‘Suspicious Activity Reports’ a Turance, da kuma wadanda su ka damka wa Gwamnatin Amurka rahoton, na harkokin wadannan shugabanni, sun kai dala tiriliyan 2 ($2,099584,477,415.49).

BuzzFeed, gungun ‘yan jaridar Binciken Kwakwaf ne su ka fallasa wadannan bayanai da aka binciko cikin kasashe sama da 170.

Me Aka Bankado A Najeriya?

Cikin daya daga irin wadannan rahotannin, an gano cewa an karkatar da dala $1,018,500 a ranar 5 Ga Maris, 2012 daga Habib Bank Limited, a reshen sa a ke New York, HBLNY.

An karkatar da kudaden ta Guemsey Trust Company Nigeria Limited (GTCL), da sunan kudaden Tanjay Real Estate Brokers ke da su.

Wannan kamfani GTCL ya na da asusun ajiyar kudade a Habib Bank Limited, reshen Dubai.

Alakar sa da Atiku ce ta sa aka yi zargin cewa shi ne ya karkatar da kudin ta Bankin HBNLY.

GTCL kamfanin Atiku ne, wanda aka yi wa rajista cikin 2003. Akwai hannun jarin babban kamfnin sa Intels a ciki har kashi 16% na Intels Nigeria Limited din a ciki. Intels kamfanin da ne mai hada-hadar kasuwanci da dama. Amma ya fi karfi wajen hada-hadar danyen fetur da gas.

Shi ne kamfanin da ya shafe shekaru hudu ya na tafka rikici da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya.

Bayan Atiku ya zama Mataimakin Shugaban Kasa cikin 1999, sai ya tattara harkokin kasuwancin sa a karkashin Intels ya yi hadin-guiwa da Gabrielle Volpi, Akintola Kekere da Uyiekpen Osagie a matsayin su ne daraktoci da amintattun kamfani, shi kuma ya ja baya daga kasuwanci ya maida hankali kan shugabanci.

“Wani bincike yw nuna cewa cikin Maris 2012 an karkatar da milyan $10 ta wasu bankuna a Amurka, a matsayin kudaden Atiku daga rahoton HBLNY.

Cikin 2010 Majalisar Dattawan Amurka a karkashin wani kwamiti ta binciki hada-hadar Atiku da Volpi. Sun yi zargin manyan shugabannin siyasa na karkatar da kudade cikin Amurka.”

Daga cikin dala milyan 40 da binciken Kwamitin Majalisar Dattawan Amurka sun gano an karkatar da sunan Atiku, dala milyan 25 duk a cikin bankunan Amurka aka shigar da kudaden.

Bankunan sun kai 30 da aka kimshe kudaden a ciki, kuma duk matar Ariku ta hudu, mai suna Jennifar Douglas ce ta bude asusun ajiyar da aka dankara kudaden a wadannan bankuna 30.

Ba wanann harkallar kadai ce aka binciko da aka danganta ko alakata ta da Atiku ba. Akwai su dalla-dalla kuma tiryan-tiryan a cikin wadannan fayil-fayil na fallasar harkallar manyan kudade a kashashen waje da aka zargi manyan ‘yan siyasar Najeriya na aikatawa.

Kakakin Atiku Paul Ibe ya ki cewa komai bayan da PREMIUM TIMES ta tuntube shi da wadannan bayanai.

Share.

game da Author