KADUNA: Mahara sun sako mai jego da jarinta da wasu 8, mutum 10 na tsare

0

Maharan da suka yi garkuwa da ƴan gida daya a Kaduna sun sako wasu daga cikin su da ya hada da wata mata mi jego da jaririnta da kuma wasu kananan yara da suka arce dasu.

Kamar yadda waɗanda aka sako su ka faɗi, sunce maharan sun umarce su da su sanar wa ƴan uwan su cewa ba za su sako sauran ba sai an ba su kudin fansa naira miliyan 15.

Idan ba a manta maharan sun kai harin samame da mahara suka kai Garin Udawa da ke Karamar Hukumar Chukun ta Jihar Kaduna, sun arce da mutum 17 bayan sun damke wata maijego da jinjirin da ta ke shayarwa.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar su ta zuwa gona, a kusa da Gonar Lema.

Dukkan wadanda aka yi garkuwar da su dai ƴan gida ɗaya ne.

Daya daga cikin wadanda suka dawo gida wanda shi mamayar ƴan ta’addan ne yayi ya waske ba su sani ba ya shaida cewa saida tafiyar Awa takwas a ciki daji kafin ya iso gida.

Mai unguwar garin Mohammed Hussaini, ya bayyana cewa akwai wadannan mutane da mahara suka sace talakawa ne fitik, basu da abincin yau ballantana na gobe.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna Mohammed Jalige bai amsa waya da aka yi masa don samun karin bayani a kai.

Share.

game da Author