A wani harin samame da mahara suka kai Garin Udawa da ke Karamar Hukumar Chukun ta Jihar Kaduna, sun arce da mutum 17 bayan sun damke wata maijego da jinjirin da ta ke shayarwa.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar su ta zuwa gona, a kusa da Gonar Lema.
Dukkan wadanda aka yi garkuwar da su dai ‘yan gida daya ne, wadanda aka tsere da su a ranar Asabar.
Kafin a gudu da su dai sai da Ƴan bindigar suka kashe mutum ɗaya, kuma suka ji wa huɗu rauni.
“Wadanda aka ji wa raunin duk ‘ya’yan Yakubu Gurmi ne, wanda yanzu haka ya na kwance Asibitin Birnin Gwari ya na jiyyar harbin da aka yi masa.
“An kuma ji wa Blessing Yakubu da Omega Yakubu da Baby Yakubu rauni. Su ma duk su na kwance a asibitin Birnin Gwari.”
Haka Mai Unguwar yankin Yakubu Hussaini ya shaida. Sannan kuma ya ce cikin wadanda aka ji wa raunin an tabbatar da mutum daya ya mutu.
“Ita kuma maijego da aka gudu da ita da jinjirin ta, sunan ta Abigail. Har yanzu kuma babu labari.
A Jihar Kaduna dai mahara sun fi kai farmaki a Karamar Hukumar Chukun a kwanan nan.
A can ne aka sace daliban sakandare biyar a lokacin da suke rubuta jarabawar WAEC. Aka hada tare da malamin su, ciki Agusta.
Mahara sun nemi a biya fansar naira milyan 20 kafin su sake su. Har yanzu dai su na daji a tsare, ba a kubutar da su ba, bayan sace su da aka yi tsawon wata daya kenan.
Ba a samu jin ta bakin Kakakin ‘Yan Sandan Kaduna da Kwamishinan Harkokin Tsaro na Kaduna, Samuel Aruwan ba.