Kada Gwamnati ta ɗauki rahoton ɓullar sansanonin Boko Haram a kewayen Abuja abin wasa -Tsohon Daraktan SSS

0

Tsohon Mataimakin Daraktan Hukumar SSS, Dennis Amachree, ya bayyana cewa bai kada Gwamnatin Tarayya da Hukumomin Tsaron Kasar nan su yi sako-sako da labarin bullar Boko Haram a cikin dazukan Abuja, Kogi da Nasarawa.

Gargadin ya biyo bayan fallasa wata takardar sirri ce mai dauke da suna da sa hannun Mataimakin Kwanturola na Kwastan, H. A. Sabo.

Takardar ta nuna cewa akwai bayyanar ‘yan Boko Haram a Tsakiyar Najeriya, wato jihohin Kogi, Nasarawa da kuma Abuja, babban birnin tarayya.

Wannan wasika ta tada hankalin jama’a da dama a kasar nan, musamman daidai yanzu da mahara da kuma masu gsrkuwa da mutane da sauran ‘yan bindiga daban-daban suka hana al’ummar karkara da matafiya zaman lafiya a Arewacin Najeriya.

Kafin 2016, Boko Haram sun rika kai munanan hare-hare a Abuja, Nasarawa har ma da Neja a tsakiyar Najeriya.

Sun kai hari Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja da kuma Hedikwatar ‘Yan Sandan Najeriya.

Sun kai mummunan harin bama-bamai a Nyanya, kusa da Babban Birnin Tarayya Abuja. Kuma sun dasa bam a babbar Plaza din hada-hadar kasuwancin nan ta Wuse 2, wato Banex Plaza, a Abuja.

Shi dai tsohon Mataimakin Daraktan SSS, Amachree, ya ce ya kamata a jami’an kwastan su tabbatar sun zakulo wanda ya fitar da takardar har duniya ta sani.

Sannan kuma ya ce batu na sirri irin wanda ke magana kan mabuyar Boko Haram, ba abin da za a rika kara-kainar wasiku a kan sa ba ne, har ana bayyana sunaye.

Sannan kuma ya ce run farko ma babban kuskure ne da wani babban jami’in kwastan ya rubuta wasikar

“Kamata ya yi kwastan su sanar da Jami’an SSS kawai, su kuma su ci gaba da bincike.

Ya nuna shakkun sahihancin wasikar, ya na cewa yadda aka rubuta wasikar ba haka ake rubuta wasika a yi adireshi ga wata hukumar tsaro ba.

Daga nan ya nemi a rika tuntubar juna da musayar bayanan tsaro tsakanin bangarorin tsaron kasar nan.

Tuni dai Rundunar Sojojin Najeriya ta ce jama’a su kwantar da hankulan su.

Share.

game da Author