Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ya roki Gwamnan Edo Godwin Obaseki ya yafe wa Adams Oshiomhole tunda dai ya lallasa shi, ya yi laga-laga’, shi da dan takarar sa Pastor Ize-Iyamu a zaben gwamnan jihar Edo.
Wike ya yi wannan roko ne a ranar Laraba, lokacin da Obaseki ya kai masa ziyarar nuna godiya dangane da rawar da ya taka wajen ganin PDP ta yi nasara a zaben.
Wike shi ne Daraktan Kamfen na Yakin Neman Zaben Obaseki, yayin da Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ne gogarman yakin neman zaben Ize-Iyamu, dan takarar da Oshiomhole ya tsaida.
Zaben ya yi zafi maruka, biyo bayan cewa Obaseki na PDP ya samu matsala ne daga APC, inda Oshiomhole ya yi ruwa da tsakin hana shi takara karo na biyu, shi kuma ya tuma tsalle zuwa PDP.
Wike ya ce ya yi murna da al’ummar jihar Edo su ka nuna halascin zaben Obaseki. Hakan inji ya kara wa PDP karfi a yankin Kudu maso Kudu, yadda babu wata jiha a karkashin APC a yankin, duk PDP ce.
Daga nan sai ya ce a yanzu dai duk wasu ko wani gungun da su ka hana Obaseki tsayawa takara a APC, ya rigaya ya kunyata su. Don haka ya kauda kai ya yafe musu kawai, tunda dai ya shiga a gaban su yanzu.
Obaseki ya ce ya zama dole ya je Ribas ya nuna godiya ga Wike da sauran mambobin kamfen din zaben sa, domin sun taimaka masa maruka wajen kunyata wadanda su ka nemi yi masa tsirara a kasuwar siyasar Najeriya.
Obaseki ya na tare da rakiyar matar sa Besty, Mataimakin Gwamna Philip Shaibu da matar sa Maryam, sai kuma mambobin kamfen din sa, a karkashin jagoran su Dan Orbih.