JIGAWA: Mata sun siya motar asibiti don dawainiyar marasa lafiya a kauyen Baddo

0

Mata mazauna kauyen Baddo karamar hukumar Taura jihar Jigawa sun tara taro, sisi sun siya motar jigilar marasa lafiya da mata masu ciki zuwa asibiti.

Matan sun yi wannan kukan kura ne a dalilin kin waiwayar su da gwamnatin Badaru ta yi wajen basu kula musamman mata masu ciki.

Baya ga munin hanyoyi, wannan kauye ko cibiyar kiwon lafiya bata da shi.

A haka dai suka rika hada kudi a tsakanin su suka siya wannan mota domin cigaban su.

Gwamnati na biyan mata Naira 5,000 duk wata na tallafi a kauyen da horas da su sana’oin hannu.

Sun rika bada naira 1000 duk wata cikin tallafin naira 5000 da gwamnati ke basu duk wata a tsakanin su.

A haka a haka dai suka tara naira 900,000, daga nan kuma sai suka samu gudunmawar naira 100,000 duk dai su hada aka sayi motar.

Shugaban kungiyar matan kauyen Baddo Hanne Hassan ta bayyana cewa siyan motar ya taimaka matuka wa mutanen kauyen.

A duk lokacin da mace ta fara nakudar haihuwa, maigida sai ya dauki motar ya dan yi direban Ihsani da kudin mai ya kai su asibiti da ke nisan kilimita 30 daga kauyen.

“Mulkin tsohon gwamna Sule Lamido ya taimaka wajen samar da motar daukan marasa lafiya daga kauyen zuwa asibiti amma bayan haɗari da motar tayi ta lalace sai yanzu muka iya siya wa kan mu.

Matakan inganta kiwon lafiyar mata da gwamnati ta dauka a jihar.

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Kabiru Ibrahim ya bayyana cewa gwamnati ta tsara shirin inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana Wanda ke aiki a jihar sama da shekara 20.

Ya ce domin farfado da Shirin gwamnati ta horas da direbobi 1,000 daga kungiyar direbobi kan yadda za su taimaka wajen jigilar mutane musamman mata masu zuwa asibiti.

Share.

game da Author