JIGAWA: Jami’an tsaro sun damke dan shekara 30 da ya yi wa ƴar shekara 5 fyade

0

Rundunar Sibul Dufens ta kama wani dan shekara 30 da ya tabbatar da bakinsa cewa ya yi wa wata ƴar shekara biyar fyadi a gidan sa.

Kakakin rundunar tsaro na Sibul Difens Adamu Shehu ya shaida haka a wata takarda da ya rabawa mabema labarai a garin Dutse.

Habibu ya ce a cafke wannan mutum mai suna Habibu Mohammed a unguwar Gabas, dake karkana, karamar hukumar, Yankwashi dake jihar.

Mahaifin yarinyar ne ya kawo kara ofishin su.

” Mahaifiyar ƴainyar ta ce yarinyar ta gaya mata cewa gaban ta na yi mata ciwo bata iya tafiya sosai, daga nan sai ta ce ta cire kaya ta ga me nene a wurin. Bayan ta duba sai ta ga anji mata ciwo a gaban nata. Da ta tambayi yarinyar sai ta ce mutumin ya ce idan ta fadi zai kashe ta.

” Sannan ta fadi cewa Habibu ne ya aikata hakan.

Bayan an kama Habibu, ya bayyana wa jami’an tsaro cewa da farko dai ya kirata gidan sa don ya aike ta ne amma kuma da ta zo sai ya canja shawara yayi nuna fin karfi yayi abinda ya ga dama.

Tuni dai rundunar ta mika cigaba da bincike akan abinda ya faru ga Hukumar binciken laifuffuka irin haka.

Jihar Jigawa dai ta yi kaurin suna wajen samun laifuffuka irin haka a kasar nan.

Share.

game da Author