Manyan Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC sun jingine yajin aikin da zanga-zangar da su ka shirya farawa daga yau Litinin, 28 Ga Satumba.
Sun jingine zanga-zangar bayan yarjejeniyar da su ka cimma tsakar daren ranar Lahadi tare da Gwamnatin Tarayya, a ganawar da su ka yi a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya sanar da janye yajin aikin da kuma yarjejeniyar da bangarorin biyu su ka cimma.
Ga Yarjejeniyar Da Aka Rattaba Wa Hannu:
1. An amince a jingine karin wutar lantarki, amma a kafa kwamitin da zai hada har da wakilan NLC da TUC, wadanda za su tattauna lamarin nan da makwanni biyu, daga yau Litinin.
2. Za su yi nazarin halacci, cancanta ko kuma haramci da rashin cancantar karin kudin lantarkin.
3. Kwamitin nazarin kudin lantarki zai kunshi:
Karamin Minsiatan Kwadago, Festus Keyamo (Shugaban Kwamiti).
Karamin Ministan Harkokin Lantarki, Godwin Jedy-Agba.
Shugaban Hukumar Kayyade Kudin Wutar Lantarki, James Momoh.
Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a Fannin Ayyukan Raya Kasa, Ahmed Zakai.
Mamba daga Kungiyar NLC, Onoho Ebhohimhen da Joe Ajaero.
Mamba daga Kungiyar TUC, Chris Okonkwo.
Wakiki daga Kamfanonin Saida Wutar Lantarki (Discos).
Yarjejeniya Kan Karin Kudin Fetur:
4. Bangarorin sun amince a fadada yawan man da ake tacewa a cikin gida Najeriya, domin a rage dogaro da shigo da tataccen fetur daga waje a ko da yaushe.
5. NNPC ta gaggauta karasa aikin gyaran matatun mai na Fatakwal, Warri da Kaduna, yadda nan da watan Disamba, 2021 akalla za a kammala kashi 50 bisa 100 na gyaran matatar Fatakwal.
6. Sauran matatun Warri da ta Kaduna kuma nan ba da dadewa ba za a bayyana wa’adin da za a bayar domin a kammala gyaran su, har su fara aiki.
7. Za a shigo da Shugabannin Kungiyoyin NUPENG da PENGASSAN a cikin Kwamitin Nazarin Fetur din.
8. Gwamnatin Tarayya za ta fara shirin ganin yadda za daina cire haraji daga albashin masu karbar mafi karancin albashi, domin rage wa masu karamin karfi jin jikin da su ke yi saboda kuncin rayuwa.
9. Gwamnatin Tarayya za ta raba wa Kungiyoyin Kwadago motocin sufuri (Mass Transit) har guda 133 a fadin kasar nan. Daga nan kuma a hankali za a raba a jihohi zuwa kananan hukumomi, kafin nan da watan Disamba, 2021.
10. Gidajen Gwamnatin masu saukin kudi da gwamnatin tarayya ke ginawa, za a saida kashi 10 bisa 100 din su ga mambobin kungiyar NLC da TUC.
11. Akwai lamuni mai tsoka daga Bankin CBN da za a bai wa mambobin NLC da TUC nan ba da dadewa ba kuma za a bayyana ranar fara karbar lamunin domin aikin noma.
Discussion about this post