Wasu mambobin jam’iyyar APC reshen Jihar Ekiti, sun zargi Gwamna Kayode Fayemi na jihar da goyon bayan Godwin Obaseki na Jihar Edo, a zaben gwamna, wanda Obaseki din ya kayar da Ize-Iyamu na APC.
Gwamnan Ekiti dai dan APC ne, kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.
Wadanda su ka zarge shi din sun ce a yanzu haka ya na kitsa tuggun da zai sa ya kore su daga jam’iyyar baki daya.
Tsawon watanni da dama kenan rikici ya tirnike jam’iyyar APC a Jiar Ekiti.
Cikin makon da ya gabata, PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa an gayyaci Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Siyasa, Babafemi Ujudu, shi da wasu cewa su bayyana gaban kwamiti domin amsa tamboyoyin dalilin rashin bin umarnin jam’iyya da su ka yi.
An nemi a ji dalilin da ya sa su ka ki janye kararrakin da su ka maka APC a gaban alkalan kotuna badan-daban.
A martanin su wanda su ka turo wa PREMIUM TIMES, sun ce babu wata jam’iyya da ta gayyace su, Gwamna Fayemi ne dai kawai kanwa-uwar-gamin gayyatar su din da aka yi.