ITF ta dira jihar Gombe, zata gina katafaren Ofis don horas da matasan yanki Arewa Maso Gabas

0

Asusun samar da tallafi ga matasa da horas dasu sana’o’in hannu, ITF zata gina katafaren ofishi a garin Gombe babban birnin jihar Gombe, domin horas da matasan yankin Arewa maso Gabashin Kasar nan sana’o’in hannu daban-daban.

Tawagar wannan hukuma ta gwamnatin Tarayya sun ziyarce garin Gombe domin yi wa gwamnatin jihar wannan albishir.

Nan take kuwa, Gwamnan jihar Inuwa Yahaya ya bada umarnin a sama wa hukumar ofishin wucin gadi kafin a gina babban ofis din a jihar.

Sannan kuma ya umarci mataimakin gwamnan jihar ya samar wa hukumar fili mai fadin Hekta 4 domin gina ofishinta na dinindin da wuraren koyar da sana’a dabandabam har guda 7.

A jawabinsa ga tawagar ITF gwamna Inuwa ya ce da kansa yayi tattaki zuwa ofishin samar da ayyukan yi ta Kasa, NDE, ya roki su garzayo jihar domin koyar da matasan jihar sana’o’in hannu.

” Wannan ziyara da kuka kawo mana da wannan albishir abin farinciki ne matuka a garemu domin hakan ya gagara a baya duk da an yi ta kokarin a samu hakan.

” Sakaci da gwamnatocin baya suka yi na kin maida hankali wajen samar wa matasa abin yi ta hanyar bada karfi wajen koya musu sana’o’in hannu yayi sanadiyyar barkewar rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Gabas da kuma kasa baki naya.

A karshe shugaban tawagar wanda babban darekta ne a hukumar, Mohammed Ningi, ya shaida cewa wannan ofishi da za a gina a Gombe zai zamo irinsa na farko a wannan yanki.

Daga nan sai ya cigaba da yaba wa gwamna Inuwa kan maida hankali da yayi don ganin ya inganta rayuwar matasa a jihar. Ya kuma kara da yin kira ga sauran gwamnoni su yi koyi da shi.

Share.

game da Author