INA MASOYAN BUHARI: Ku turo min da naira Dubu ɗai-ɗai zan yi Buhari sabuwar waka – Rarara

0

Fitaccen mawaƙin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da jam’iyyar APC, Dauda Kahutu, da aka fi sani da Rarara ya yi kira ga masoyan shugaban Kasa Muhammadu Buhari su tara masa kudi yayi wa Buhari waka.

Rarara ya faɗi haka ne a bidiyo da ya fitar ranar Alhamis wanda ya saka a shafin sa ta Instagram ya na shelar cewa duk mai ƙaunar Buhari ya tura masa naira 1000 ya yi wa Buhari waka.

‘Ana cewa farin jinin Buhari ya ragu. Toh ina so mu nuna wa mutane cewa farin jinin sa ma ƙaruwa yayi.

” Saboda da haka ina shirya waƙan da zan lissafo ayyuka masu ɗinɓin yawa wanda Buhari ya gama da su cikin shekara ɗaya a wannan zango da muke ciki.

Daga nan sai mawakin ya faɗi asusun ajiyar sa na banki da za a saka kuɗin a ciki domin ya haɗa wakar kowa ya ji.

Sai dai kuma saka wannan sako tasa ke da wuya wasu masu yin sharhi a yanar gizo suka ragargaje shi yadda suke so.

Da yawa daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakin su akai sun soki abin ƙarara inda suke cewa Rarara dai maula kawai yake yi amma in Kuɗin waka ya ke nema ya san inda zai neme su.

” A wannan yanayi da ƴan Najeriya ke cikin matsaloli da matsin rayuwa saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasa, kawai sai ka wani ce a tara maka Dubu ɗai-ɗai wai don za ka yi wa Buhari waka, kada kayi mana.” Inji Habiba Baba.

” A kara mana Kuɗin man fetur, a ƙara kuɗin wuta, sannan abinci ma yanzu ya gagari mutane kawai da wani rana tsaka kace wai a tara maka Dubu ɗai-ɗai saboda waka. Ta abinci za aji sa ko waka.” Sani maska.

Haka dai mutane suka yi faɗi, sai dai wasu kuma su yabi mawakin inda suka ce soyayyace ta ke ingiza shi da abinda yake samu a wajen gwamnatin.

Share.

game da Author