Gwamnan jihar Barno, Babagana Zulum ya yi gargadi da kakkausar murya cewa dole fa jami’an tsaro su kara kaimi da maida hankali matuƙa wajen fatattakar Boko Haram da kawo karshen sa, in ba haka ba kuwa Maidugurin ma za ta koma karkashin ikon su.
Zulum ya ƙara da cewa babban burin sa shine a kawo ƙarshen ta’addancin da Boko Haram suka gallaza wa mutanen yakunan Arewacin Barno, su samu su koma garuruwan su domin su ci gaba da noma da kula da kansu da iyalansu.
Sai dai kuma duk da haka ya ce tabbass zai bi abin a hankali yanzu, saisa-saise ganin yadda sau biyu kenan yake tsallake rijiya da baya a harin da Boko Haram suke kai wa tawagarsa.
Ƴan majalisan dake wakiltar daukacin jihar a majalisar kasa dake Abuja suka kawo wa gwamna Babagana Zulum ziyarar jaje kan harin Boko Haram da ya kuskure.
Ƴan majalisan karkashin jagorancin tsohon gwamna Kashim Shettima, sun yi kira ga gwamnan da ya rika bi a hankali, saboda yadda Allah ya kubutar da shi daga harin Boko Haram har sau biyu a ƴan kwanakin nan.
” Muna kira ga mutanen gari su cigaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya domin a kawo karshen wannan matsala na tsaro a jihar da yankin Arewa maso Gabas.
” Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka rawar gani matuka wajen ganin an gama da Boko Haram, sannan kuma da abun ayaba masa ne kirkiro da Hukumar raya Yankin Arewa Maso Gabas da yayi.
A karshe sun jinjina wa gwamna Zulum bisa ayyukan cigaba da ya sa a gaba domin mutanen jihar Barno.
Discussion about this post