Hukumar Hisbah ta cafke saurayin da ya fallasa bidiyon fasikancin da ya yi da tsohuwar budurwarsa dake shirin aure

0

A ranar Talata ƙungiyar hisbah dake jihar Sokoto ta cafke wani matashi da abokanan sa biyu da ake zargin su da saka bidiyon fasikancin da daya daga cikinsu ya yi da tsohuwar budurwar sa a yanar gizo.

Wannan matashi dai tsohon saurayin wannan yarinya ne da take shirin yin aure a cikin watan Oktoba.

Kwamandan kungiyar Adamu Kasarawa ya bayyana haka a hira da yayi da BBC Hausa.

Kasarawa ya ce mahaifiyar budurwar ne ta kai kara a ofishin Hisbah.

“Mahaifiyar ta ce a shekarar 2017 lokacin ƴarta na soyyaya da matashin ne ya kai ta otel ya kwana da ita sannan bayan haka ya rabu da ita.

” Ashe a lokacin da suke otel din abokan matashin sun boye a dakin suna daukan bidiyon fasikancin da ya yi da yarinyar.

“Ba a sake ganin wannan saurayi ba sai da yarinyar za ta yi aure.

Kasarawa ya ce matashin ya saka bidiyon fasikancin da yayi yarinyar ne wai don ya bata mata suna a wajen surukanta.

Ya ce a yanzu haka saurayin da yarinyar za ta aura ya fasa auren saboda bidiyon da ya gani.

Kasarawa ya ce kungiyar ta aika da wannan matsala zuwa hukumar NAPTIP domin ci gaba da bincike.

Share.

game da Author