HATTARA JAMA’A: Dagwalon masana’antu ya kashe mutum uku a dajin ɗibar katako

0

Mutum uku sun mutum a lokacin da ruwan dagwalon masana’anta ya ɓarke daga cikin wata madatsar ruwan da ya ke kwarara ya yi gaba da su cikin wani kwatami.

Lamarin ya faru ne a cikin dajin Omotasho a Jihar Ondo, inda wasu ƴan Chana suka kafa masana’antar sarrafa rogo, falankin katako da kuma tayil na daɓen ɗaki.

Dajin Omotasho dai ya na yankin garin Okitipupa a Jihar Ondo. Jami’an ƴan sanda sun tabbatar da faruwar mummunan lamarin.

Kamfanin mai suna Wewood mallakar wasu ƴan Chana ne, wanda ruwan dagwalon da ke gangarawa cikin wata karamar madatsar ruwa, wadda mutanen garin suka gina, ya yi sanadiyyar kisan mutanen uku.

Karin bayanin da jami’an ƴan sanda suka yi, ya bayyana sunayen matattun da Akinmusire Monday, mai shekara 35, Louis Samuel mai shekara 43 sai kuma matashi Ododolewa Adebowale, mai shekara 19.

Ƴan sanda sun ce mamatan uku sun shiga daji da niyyar aikin yankan itacen katako, wato timba.

Louis shi ne Ɗan kwangilar aikin katako, shi kuma Monday shi ke da injin na yankan bishiyoyi. Adebowale kuma matashi da ke taimaka masu wurin aikin.

An ce matashin a yanzu ya ke rubuta jarabawar fita sakandare.

“Ba su sakankance ba sai ruwan dagwalon masana’anta ya ɓarke daga madatsar ruwa ya yi gaba da su zuwa cikin wani kwatami.”

An tsinci gawarwakin su a cikin dagwalon masana’anta, bayan da Basaraken Akinfosile, mai suna Olamide Ayodele ya kirawo DPO na yankin, ƴan Bijilante da kuma Dakarun Amotekun.

Kakakin Yada Labarai na Jihar, Tee Leo-Ikoro, ya tabbatar da cewa ruwan dagwalon da ya keta madatsar ruwan ne ajalin mamatan.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa ana kokarin sasantawa tsakanin iyalan mamatan da kamfanin na ‘yan Chana.

Amma kuma tuni sun ɗauki lauya wanda zai bi musu hakkin biyan diyya.

Share.

game da Author