HARƘALLAR P&ID: “Allah ya tsine wa maƙaryaci” -Raddin iyalin Rilwanu Lukman ga Minista Malami

0

Iyalan tsohon Ministan Harkokin Fetur, Rilwanu Lukman, sun ƙaryata zargin da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi wa mahaifin su cewa ya sa hannu kan kwangilar samar da gas tsakanin Najeriya da kamfanin P&ID ne don kawai amfanin kan sa.

Daya daga cikin ƴaƴan marigayin, mai suna Ramatu Lukman, ta nemi Malami ya ba iyalan mahaifin na su hakuri, bisa ga abin da ta kira ƙitsa masa ƙarairayi da sharri da Ministan Shari’a ya yi, saboda ya ga ba shi duniya, ballantana ya iya kare kan sa.

Ramatu ta ce sun yi mamakin yadda Malami ya rika kantara wa mahaifin su karairayi, ya na bata masa suna da sunan su iyalan na mamacin, shekaru da dama bayan mahaifin na su ya rasu.

Wannan kakkausan raddi ya biyo bayan zargin da gwamnatin tarayya a karkashin Minista Malami ta zargi akwai hannun Rilwanu Lukman wajen harkallar kwangilar P&ID.

Shekaru uku kenan PREMIUM TIMES HAUSA na kawo dalla-dallar wainar da ake toyawa, tun lokacin da gayyar kwangilar ta watse.

Kamfanin P&ID ya maka Najeriya kara a Birtaniya, saboda ta ki cika sharuddan kwangila, abin da ya ja aka ci tarar Najeriya cewa ta biya P&ID dala biliyan 9.6.

Kokarin kare kan ta da Najeriya ke yi don kada ta biya diyyar, ta kai Malami sanar da Kotun Kararrakin Hada-hadar Kasuwanci ta Ingila cewa su Rikwanu Lukman sun shirya kwangilar da sanin cewa hakan ba za ta yiwu ba.

Wannan zargi da ya yi wa Lukman bayan mutuwar sa, ya harzuka iyalan sa, har suka kasa daurewa tsawon lokaci suka fito da raddi a yanzu.

“Ka na yi wa mahaifin mu karairayi saboda ka san ba ya duniya, ba zai iya kare kan sa ba.

“Idan kai ne iyalin sa ya za ka ji damuwar irin wannan zubar da kima da ake yi maka?”

“To mu na tuna maka irin tsinuwar da Allah ya yi wa makaryaci da kuma fushin da ya ke yi da shi mai karyar a cikin Alkur’ani, Suratul AZZUMAR, Aya ta 3:

“Allah zai yi hisabi a tsakanin su daga abin da su ka bambanta a kai. Amma Allah ba zai shiryi makaryaci kuma marar godiya ba.”

Zargin Da Malami Ya Yi Wa Lukman A Kotun Birtaniya:

“Rilwanu ne ya umarci hadimin sa mai suna Taofiq Tijjani cewa kada ya yi la’akari da rashin cancantar kamfanin P&ID, ya ci gaba da tsara kwangilar kawai.

“Tijjani ya shaida wa masu bincike daga EFCC cewa Lukman ya ba shi umarnin tsara kwangilar da P&ID, duk da cewa ba su san komai a harkar gas ba.

“Karamin Ministan Harkokin Fetur a lokacin, wanda harkar kwangilolin da suka shafi gas ke karkashin sa, ya ce Lukman ya kife shi, ba da shi aka shirya bada kwangilar ba.”

Malami ya kara shaida wa kotu cewa:

“Kamfanin P&ID da ke Tsibirin British Virgin Islands, ya bayar da cin hancin dala 390,000 a 2012, bayan an ba shi kwangilar cikin 2009.

Hukuncin Kotu:

Kamfanin P&ID ya kai Najeriya kara, cewa ya kashe dala milyan 40 wajen fara aiki. Amma Najeriya ta kasa gina ayyukan da yarjejeniyar kwangilar ta ce sai ta gig-gina sannan P&ID zai iya ci gaba da aiki.

Kotu ta ci tarar Najeriya dala bilyan 9.6. An ce ko ta biya, ko kuma a debi kudin cikin asusun Najeriya da ke kasashen waje.

Ba wannan ne karon farko da aka tarbi Malami gaba-da-gaba a kan batun harkallar kwangilar P&ID ba.

Cikin Agustan jiya, PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa, tsohon Ministan Shari’a, Mohammed Adoke ya maka Minista Malami kara a kotun Landan.

Tsohon Ministan Shari’a Mohammed Adoke, ya maka wanda Ministan Shari’a Abubakar Malami a wata kotu da ke Landan, bisa zarfin gabatar da takardun shaida na karya a kan sa, yayin dambarwar shari’ar harkallar kudade ta kamfanin P&ID.

A cikin takardar sammacen karar, wanda PREMIUM TIMES ta ci karo da su, Adoke ya nemi Malami ya janye takardun bayanan shaidar da ya bayar kan Adoke din a shari’ar harkallar P&ID.

Harkallar P&ID ta fito fili a shekarar da ta gabata, yayin da wata Kotun Birtaniya ta yanke wa Najeriya hukuncin diyyar dala bilyan 9.6 ga kamfanin P&ID, saboda karya yarjejeniyar kwangila kafa bututun gas.

Kwatagwangwama ta harde yayin da kotu ta ce ba za ta soke hukuncin biyan diyya da Gwamnatin Najeriya ta nemi kotun ta yi ba, har sai Najeriya ta tabbatar mata cewa dama can kwangilar ta gidoga da harkalla ce aka shirya, an san ba mai yiwuwa ba ce.

Kwangilar dai an rattaba mata hannu cikin 2010, zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Umaru ‘Yar’Adua, lokacin da ya ke jiyya a asibitin Saudi Arabiya.

Cikin karar da Adoke ya shigar, ya yi Ikirarin cewa abubuwan da Malami ya mika wa kotu a kan sa, duk kage ne da kuma sharri.

Adoke ya roki kotu ta cire yananan shaida ta 4 da Malami ya gabatar wa kotu a ranar 5 Ga Disamba, 2019.

Ya kuma nemi gwamnatin tarayya ta cire bayani na sadara ta 11.4, na 23 da 24.4 da aka shigar a kotu, a ranar 5 Ga Disamba, 2019.

Sai kuma bayanan da Malami ya shigar a ranar 6 Ga Maris, na sadara ta 19.3, na 105.1, na 105.4, na 112, 114.2, na 114 da kuma na 115.58.

Babban lauya Paul Erokoro ne lauyan Adoke, kuma shi ne lauyan James Nolan na kamfanin P&ID.

PREMIUM TIMES ta sha buga rahotannin musamman akan wannan dambawar kwangilar da ba a aiwatar da ko Kashi 1% bisa 100% ba, amma ake neman Najeriya ta biya diyyar dala bilyan 9.6.

Share.

game da Author