Hukumar jindaɗin Alhazai na jihar Kaduna ta fara maida wa Alhazan da suka biya kudin aikin hajin bara kudin su.
Shugaban hukumar Hannatu Zailani ce ta sanar da haka a lokacin da take hira da manema labarai a garin Kaduna.
Hannatu ta ce mutum 188 daga cikin mutum 2,383 da suka biya kuɗin Hajjin suka nemi a basu kuɗin su kawai.
Ta ce wadanda ba su karbi nasi kudin ba za a cigaba da ajiyewa har sai an biya aikin hajjin su ba za a ajiyan kudin zuwa na badi.
Jannatu ta kara da cewa duk wanda ya karbi kudin sa to daga farko zai fara idan shekara ta zagayo.
A ƙarshe ta roki masu karɓar kudin su kiyaya sharuddan dokar Korona, kada su gwamatsu sannan su saka takunkumin fuska.
Idan ba a manta ba a watan Yuni Ma’aikatan aikin Haji ta kasar Saudi Arabiya ta sanar cewa baki ba za su halarci kasar domin yin aikin Haji a bana ba.
Ma’aikatar tace wadanda ke zaune a kasar ne kawai za su yi aiki tare da ƴan kasar Saudiyya amma ba bu baki da ga wasu kasashe da za su shigo kasar domin yin aikin Haji.
Har yanzu dai annobar Korona bai rabu da mutanen duniya ba. Ba a san yadda za ata kasance ba a shekara mai zuwa game da aikin Hajji din.
Discussion about this post