Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin fito da shirin Yaƙi Da Yunwa, wato Zero Hunger Round Table, don rage wa al’ummar Najeriya raɗaɗin fatara da yunwa.
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Kyautata Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq, ita ce ta bayyana haka a wajen taron Cibiyar Samar Da Abinci ta Kasa (National Food Security Council) wanda aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A jawabin da ta gabatar a taron, Hajiya Sadiya ta bayyana cewa za a fito da shirin ne a matsayin wani bangare ne na kokarin da ma’aikatar ke yi na rage yunwa a Nijeriya, wadda zaman dole na annobar korona ya kara kambamawa, da nufin kawar da yunwa tare da samar da abinci, inganta samar da abinci mai gina jiki da kuma habaka aikin gona ya zuwa shekara ta 2030 tare da hadin gwiwar wadanda abin ya shafa.
Ta ce: “Wannan Ma’aikatar ta samar da hanyoyin rage wa jama’a radadin matsalolin rayuwa ta hanyar samar da abinci cikin gaggawa da kuma hanya mai dorewa ta hanyar shirin Magance Yunwa.
“A matsayin daya daga cikin ayyukan wannan Ma’aikata na tabbatar da rage radadin aukuwar bala’o’i tare da shirin ko-ta-kwana da kuma kai agaji, shirin Inganta Rayuwar Al’umma na Kasa (NSIPs) ya taimaka wa aikin Ma’aikatar a matsayin wata hanya ta samar da hanyoyin taimakon jama’a, ciki har da bada abinci ga mutane marasa galihu a dukkan fadin kasar nan.”
Sadiya ta tuno da cewa shirin nan na ciyar da ‘yan makaranta da ke zaman gida da na kai abinci gida (Take Home Rations, THRs) an yi su ne domin samar da abinci ga gidaje mabukata guda 127,589 masu yara ‘yan aji 1 zuwa 3 na firamare a makarantun gwamnati a Yankin Babban Birnin Tarayya (FCT) da jihohin Legas da Ogun, yayin da aka kai manyan motoci 164 shake da kayan abinci a jihohi 36 da yankin Abuja a matsayin agaji da aka samu daga Hukumar Kwastam ta Nijeriya.
Ta kara da cewa, Ƴa zuwa yau dai, sama da tan 41,000 na hatsi daga Rumbunan Ajiyar Hatsi da ake sa ran za su kai ga gidaje sama da miliyan 5 aka mika wa gwamnatocin jihohi 19 da Babban Birnin Tarayya. Ana rabon ne ta hanyar hukumar NEMA a bisa umarnin Shugaban Ƙasa.”
Ministar ta kara da cewa Shirin Yaki Da Yunwa za a yi shi ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Aikin Gona da Habaka Karkara ta Tarayya da kuma wasu shugabannin kamfanoni masu zaman kan su irin su Tony Elumelu, Tonye Cole da kuma Sahel Consulting, IFPRI, IITA, NESG, FAO, IMMAP, ECOWAS da sauran su.
Ta bayyana cewa hanyoyin da za a bi a aiwatar da wannan Shirin Yaki Da Yunwa din sun hada da yin amfani da bayanan da aka tattara game da gidajen da ke bukatar taimako, da hadin gwiwa, samar da aikin yi da kuma taimaka wa sashen aikin gona tare da inganta hanyoyin da abinci ke bi daga manoma ya kai ga masu sayar da shi, da inganta samar da abinci mai gina jiki, Ƙarfafa rumbunan tara abinci tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Aikin Gona da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin.