Gwamnatin Jihar Neja ta kori ma’aikata 80 da suka riƙa karɓar alawus ɗin da ba na su ba

0

Gwamnatin Jihar Neja ta rattaba hannun amincewa a kori wasu ma’aikatan gwamnatin jiha, wadanda aka samu da laifin karbar alawus-alawus din da ba na su ba.

Wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Neja ta buga a shafin ta na Twitter, ta bayyana wa manema labarai wannan kora da aka yi wa ma’aikatan bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta Jiha.

Da ta ke bayanin laifukan da suka yi har aka sallame su, Shugabar Ma’aikata Salamatu Abubakar ta shaida wa manema labarai cewa gwamnati ta kafa kwamitin da zai binciki tsarin albashin wadanda aka korar din.

Salamatu ta ce ma’aikatan da aka kama da laifin akwai 1 daga Ma’aikatar Ilmi, 45 daga Hukumar Kula da Asibitoci, 3 daga Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jiha, 7 daga Ma’aikatar Lafiya, 1 daga Makarantar Koyon Aikin Jiyya ta Jiha.

Akwai kuma 22 daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Neja.

An gano sun dora kan su a kan mataki na albashi wanda ya zarce abin da ake biyan kowanen su a ka’idar albashin sa.

Bayan an kafa musu Kwamitin Bincike ne sai Kwamitin Binciken ya bada shawarar a sallami dukkan su, su 80 din
“Kwamiti ya kira kowanen su. Kuma sun tabbatar da aikata laifin da ake tuhumar su. Yanzu haka takardar korar su daga aiki na nan ana shirin damka masu.”

Gwamnatin Jihar Neja din kuma ta ce Kwamitin Binciken na nan na ci gaba da aiki. Duk baragurbin da aka kama, za a kore shi kawai.

Share.

game da Author