Jam’iyyar APC ta ce Gwamnatin Tarayya ta ƙara farashin wutar lantarki da na man fetur domin jin daɗin ƴan Najeriya.
Wannan bayani ya fito ne a matsayin raddi ga jam’iyyar PDP, wadda a ranar Laraba ta shiga sahun ƴan Najeriya masu sukar ƙarin farashin fetur da na hasken lantarki.
Cikin sanarwar da PDP ta fitar a ranar Labara bayan gwamnati ta fito da sabon farashin sarin litar fetur naira 151 daga NNPC, jam’iyyar PDP ta ce ba ta yarda da karin ba.
“Kun ce a kori PDP saboda a gwamnatin ta ana saida fetur naira 87. To ga shi nan a karkashin APC, tun ba a je ko’ina ba lita daya ta koma naira 161.” Inji PDP, cikin sanarwar da Kakakin Yada Labarai Kola Olagbondiyan ya fitar.
Gwamnatin Buhari ta kara kuɗin fetur kwanaki biyu bayan nunka kudin wutar lantarki daga naira 30.36 mitar wuta daya, zuwa naira 66 mita daya.
A na ta martanin, jam’iyyar APC ta ce an yi wannan ƙari ne saboda lalubo hanyoyin da ƴan Najeriya za su samu sauƙin rayuwa.
A sanarwar da Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai, Yekini Nabena ya fitar, APC ta ce duk wannan galauniya da ake fama da ita, ta samo asali ne daga matsalar da mulkin PDP na shekara 16 ya jefa Najeriya.
“Rashin kunya ce da PDP ta fito ta na sukar karin farashin fetur. Domin ita ce silar shigar Najeriya cikin wannan matsalar. Me zai hana su dawo da kudaden tallafin man fetur ɗin da suka danne a tsawon shekaru 16 su na mulki.”
Tuni dai wannan kari ya haifar da maganganu, har mutane da dama na tuna mulkin Jonathan.
Karin farashin fetur da na wutar lantarki, ya zo a daidai lokacin da tsadar kayan abinci na neman abincin ya gagari talaka a Najeriya.