Gwamnati za ta tsara hanyoyin kaiwa da raba kayan agaji a Arewa Maso Gabas

0

Gwamnatin Tarayya za ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai samar da hanyoyi mafi sauki da za a riƙa kai agaji ga waɗanda rikicin yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya ya shafa.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Kyautata Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq, ita ce ta bayyana haka a cikin wata takardar bayani ga manema labarai a Abuja ran Litinin.

A cewar ta, rashin samun kaiwa ga jama’ar da rikicin ya shafa wani babban abin damuwa ne.

A takardar, wadda hadimar musamman kan yaɗa labarai ta ministar, Nneka Anibeze, ta rattaba wa hannu, Sadiya Farouq ta ce kula da tsaron lafiyar ma’aikatan agaji a Arewa Maso Gabas shi ma tarnaki ne ga aikin kai kayan agaji ga masu bukata.

Ta ce: “Guruf ɗin ma’aikatan da za a nada za su fito da ingantacciyar hanya wadda dukkan mu za mu yi amfani da ita a matsayin ma’aikatan agaji, wanda ya hada da jami’an tsaro, saboda mu yi aiki kafada da kafada da juna cikin sauƙi.

“Aikin mu dai na haɗin gwiwa ne, domin kowannen mu ya na bukatar abokin aikin sa don tabbatar da aikin mu ya cika.

“Don haka, ma’aikatar mu ta na ƙokarin ta ga ta kafa wani kwamiti a matakan jihohi da na tarayya wanda zai tabbatar da aikin ya gudana a Arewa Maso Gabas.

“Zai kuma hada gwiwa da ma’aikatu da sassan su da cibiyoyin su don ganin aikin raba agaji ya na tafiya yadda ya kamata.”

Ministar ta kara da cewa za ta tabbatar da cewa a wurin ma’aikatar ne za a samu duk wani abu da ake bukata saboda aikin raba agaji ya tafi daidai, ciki har da kai ziyara jefi-jefi a yankin na Arewa Maso Gabas.

Ta kara da cewa ma’aikatar za ta ria samun rahoton wata-wata ta hannun kodineta mai kula da aikin agaji a yankin (OCHA).

Hajiya Sadiya ta ce za a rinka kai kayan abinci da wanda ba na abinci ba zuwa dukkan wuraren da abin ya shafa masu wuyar shiga idan an binciko su.

“Wuraren da za a iya shiga da mota, sojoji ne za su raka mu, yayin da su kuma wuraren da ke lungu sosai za a yi amfani da jiragen Rundunar Sojin Sama ne ana cilla wa mutane kayan agajin zuwa kasa inda za su dauka.

“Saboda haka, dukkan mu tilas ne mu yi aiki tare da gwamnatocin jihohi, sojoji, Majalisar Ɗinkin NEMA, SEMA da ma wasu don tabbatar da cewa an kai kayan agajin ga mabuƙata.”

Share.

game da Author