A zaman Majalisar Zartaswa na ranar Laraba, Gwamnatin Tarayya ta amince ta kashe dala bilyan 1.9 wajen gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi da ke Jamhuriyar Nijar.
Titin jirgin zai ratsa Kano-Jigawa-Katsina zuwa Jamhuriyar Nijar.
Za a kashe dala 1,959,744,723,72, kamar yadda Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana.
Ministan ya ce a wannan adadin makudan kudade da za a kashe, an lissafa har da kudin harajin Jiki-magayi na kashi 7.5% a ciki.
Majalisar Zartaswar ta amince da a kashe wadannan kudaden ne a taron ta da aka gudanar ta Intanet, daga gida, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, a fadar sa ranar Laraba.
An ruwaito cewa Ma’aikatar Sufuri za ta kashe naira bilyan 3.049 wajen zanawa, gwaji da kuma kaddamarwa.
Run cikin 2018 Shugaba Buhari ya saka batun Gina titin jirgin kasa din a cikin kasafin 2018.
Sai dai kuma aikin da gwamnatin Buhari ta fara kaddamarwa na titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano, har yau ba a fara ba, bayan an shafe shekaru uku ana aikin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan, amma har yau iyakar aikin Abeokuta kadai.
Akwai hanyar jirgin kasa da gwamnatin Buhari ta ce za ta farfado da ita daga Fatakwal zuwa Maiduguri. Ita ma ba a yi komai ba.