Kodinatan kwamitin yaki da cutar korona na kasa Sani Aliyu ya bayyana cewa gayyana cewa gwamnati ta kara tsawon lokacin walwala yanzu daga 12 na dare ne zuwa 4 na asuba.
“Wanna doka bai hada da ma’aikatan da ya zam musu dole su fita aiki ba akamr masu dakon abinci, likitoci da nas nas.
Makarantu, gidajen cin abinci da Otel
Otel za su ci gaba da aiki tare da kiyayewa daga kamuwa da yada cutar.
Za a bude wuraren shakatawa amma ba za su yi aiki na tsawon lokaci ba.
Gidajen saida a binci za su ci gaba da aiki tare da kiyaye
Kulub za su ci gaba da zama a rufe Sai gwamnati ta ce a bude su.
Zirga-zirgar jiragen sama na kasa-da-kasa
Za a bude shafukan biyan kudin jirgi na yanar gizo ranar 3 ga watan Satumba.
Ya kuma zama dole duk wadanda za su shigo kasar nan su yi gwajin cutar korona sannan su bayyana shaidar yin gwajin cutar a lokacin da suka shigo kasa.
Haka kuma za a bude sansanonin dalibai masu bautar kasar a fadin kasar nan da zaran makarantu sun dawo karatu.