Gwamnati ta ƙara farashin man fetur, yanzu naira 151.56 duk lita

0

Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar ƙarin farashin litar man fetur zuwa naira 151.56 daga naira 138.

Hukumar Tantance Farashin Man Fetur (DPPRA) ce ta bayyana haka ranar Laraba a Abuja.

DPPRA ta ce haka za a sha kowace litar fetur naira 151.56k cikin watan Satumba

Gwamnatin Tarayya ta shigo da wannan sabon tsarin ƙayyade farashin man fetur a kowane wata, inda ta ce a wani watan farashin ka iya sauka, wani watan kuma zai iya hawa sama, kamar yadda ya hau a yanzu.

Kwamiti ne ke zaunawa a ƙarkashin Hukumar Ƙayyade Farashin Man Fetur ta ƙasa, shi ke zama kowane ƙarshen wata ya yanka farashin da ya ke ganin za a sayi litar man fetur ɗaya a Najeriya.

Hukumar PPMC wadda ke ƙarƙashin NNPC ke da alhakin sayar da fetur din da ake sayarwa a cikin Najeriya.

Saboda haka, duk wani fetur da ake sayarwa a cikin Najeriya, to PPMC ce ke kula da sayar da shi.

Sai dai kuma ba ba kamar yadda gwamnati ta sanar bane za arika saida man a gidajen mai.

Wani mai wurin adana man fetur dake saida wa dillalai mai ya ce ” Idan gwamnati ta saida mana da mai akan naira 151.56 duk lita, sai mun biya wa duk lita harajin naira biyu sannan kuma ka biya kudin d kungiya da kudin jigila. .

” A gaskiya mai zai kai naira 160 duk lita.

Share.

game da Author