‘Yan Shi’a a fadin kasar nan, karkashin IMN, sun yi Allah wadai da yadda aka nuna su a fim din ‘Fatal Arrogance’, cewa su ‘yan ta’adda ne.
Sun kuma yi tir da babban jarumin fim din, Pete Edochie, wanda ya fito a matsayin El-Zakzaky, a fim din wanda aka shirya a Enugu.
Duk da fim din bai fito ba, amma dai wani tsakuren minti 12 da aka watsa ya haifar da tashin jijiyoyi sosai a soshiyal midiya.
IMN ta ce fim din farfaganda ce ta bata sunan ‘yan Shi’a da kuma jagoran su Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Cikin wata takardar manema labarai da Kakakin IMN, Ibrahim Musa ya turo wa PREMIUM TIMES HAUSA, mai dauke da sa hannun sa, ya ce:
“A ranar 9 Ga Satumba, 2020, wasu gajerun bidiyoyi na fim mai suna “FATAL ARROGANCE”, wanda Furodusa Anosike Kingsley Orji ya shirya a birnin Enugu suka karade shafukan sada zumunta na intanet, inda a ciki aka rika nuna mata ba suturar kirki, kamar wasu matsafa, rirrike da takubba da adduna da kwalaye da hotunan wani malami cikin rawani, su na kuma furta wasu kalmomi marasa ma’ana da sunan su na yin muzahara.
“Hakika mun kadu da ganin cewa a fim din ana kokarin kamanta Harkar Musuluncin da Jagoran ta Shaikh Ibraheem Zakzaky a matsayin ‘yan ta’adda.
“Da a ce ba wata a kasa, irin wadannan gajerun bidiyon za mu iya yin biris da su, amma ba a a irin wannan hali da gwamnatin Buhari ta ke daukar nauyin ‘yan kwangila masu yin batanci, musamman mutum irin Kuanum Terrence, wanda kowa ya san rundunar sojar Nijeriya ta dauke shi aikin yi mata farfaganda a kan bata harkar Musulunci, wacce aka san ta a tsawon shekaru da kauce wa tashin hankali duk da hare-haren takala da ake kai mata.
“A sarari ya ke ga kowane dan kasa cewa wadannan gajerun bidiyon manufarsu ita ce shafa wa Harkar Musulunci kashin kaji da nuna ta a matsayin wata Harkar tashin hankali da ta’addanci a idon duniya. Har ila yau wannan fim din da ake daukar sa a halin yanzu sunan sa ya yi daidai da littafin da Terrence ya wallafa a bara, wanda bisa kudurar Allah bai samu karbuwa ba a gun jama’a, inda a ciki aka zargi wadanda aka zalunta da jawo wa kan su zalunci. Sunan littafin da Hausa wai “Mugun taurin kai: Yadda El-Zakzaky ya rudi ‘yan Harkar Musulunci su ka kashe kan su yayin kare shi”. Daga sunan littafin ma, wautar da ke cikin sa ta bayyana a sarari.”
Kisan-kiyashin Zariya Sojoji Ke Son Binnewa – IMN
Ibrahim Musa ya ci gaba da cewa, “Harkar Musulunci a Nijeriya na kira ga kwararrun masu shirya fina-finai na Nollywood da su dubi wannan al’amari da idon basira. Idan fa masu shirya fina-finai ba su yi hankali ba, wasu batagari da ke cikin gwamnati za su iya sa su, su goyi bayan zalunci a kan wadanda aka zalunta, kamar yadda shi ne manufar fim din ‘Fatal Arrogance’. Kisan kiyashi ne fa aka yi a Zariya a Disamban 2015, kuma ake ci gaba da yi, sannan shi ake so a lullube, a yi rufa-rufa, wai duniya ta manta da shi, alhali hakan raini ne ga kudurin Rome na kotun duniya wanda batun ke gabanta a halin yanzu.
“A tuna fa, bayan kisan kiyashin Zariya, gwamnatin Buhari ta kaddamar da wani kamfen na bata sunan Shaikh Zakzaky, Harkar Musulunci da Shi’a ta hanyar amfani da kudaden da ta karbo daga Saudiyya. An rubuta littattafai na batanci, kuma ‘Fatal Arrogance’ daya ne daga cikin su. Amma da gwamnatin ta fahimci littafin bai samu karbuwa ba wajen ‘yan Nijeriya, shi ne ta zagaya don yin amfani da dattijon masana’antar fina-finai Pete Edochie don fitar da fim din da zai canza hakikar abin da ya faru a Zariya, don su nuna wa duniya cewa su na da hujjar kisan kiyashin da suka yi, inda aka kashe rayuka sama da dubu na fararen hula ‘yan kasa.
“Sai dai da yawan ‘yan Nijeriya sun san cewa dukkanin muzaharorin neman a saki Shaikh Zakzaky da ake yi na lumana ne. Sojojin Nijeriya da ‘yan sanda ne suke mai da su na tashin hankali a duk lokacin da suka auka wa masu muzaharar, wanda a kan hakan sun kashe daruruwan fararen hula ‘yan kasa da suka hada da mata da yara. Don haka meye amfanin yada farfagandar cewa wadannan masu muzaharar suna dauke da makami da bama-bamai?
“Tarihi ba zai kyauta wa duk wani furodusan fim din da ya nemi ya canza gaskiya zuwa karya ba, don a samu hujjar kisan-gillar da aka yi wa wadanda ba su ji, ba su gani ba.
Muna son duniya, musamman ‘yan Nijeriya su shaida cewa, wannan fim din FATAL ARROGANCE, wasu za su iya amfani da shi su ta da hankali a al’ummun mu da su ke mabambanta.
“Wani salo ne na farfaganda ake so a yi amfani da shi don bata suna. Ana so a jirkita gaskiya ta zama karya, a kau da kai daga masu aikata muggan laifuka, a kuma dora laifi kan fararen hulan da aka zalunta ta hanyar bakanta su da kuma wanke azzalumai daga zaluncin su.
“Don haka muna kara yin kira ga dukkan ‘yan Nijeriya nagari da su matsa wa masu shirya fim din lamba don su dakatar da wannan mugun fim din.
A halin yanzu dai mun rubuta takardar koke zuwa ga Hukumar Tace Rina-finai ta k
Kasa da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda a kan wannan mummunan al’amari. Mu na jiran irin matakin da za su dauka, kafin mu dauki mataki na gaba.”
Yayin da Edochie ya yi ikirarin cewa bai san abin da ke cikin fim din ba, ‘yan Najeriya da dama, musamman a kudancin kasar nan sun yi masa raga-raga, su na cewa ya bari an yi amfani da shi a inda bai dace ba.
Shi ma dan fim din Hausa Yakubu Mohammed, wanda ya fito a cikin fim din, ya bayyana nadamar sa, da da-na-sani kan fitowar sa a fim din.
An rika jefa wa Edochie bakaken kalamai a soshiyal midiya, ana cewa ya zubar da mutuncin sa a kan kudi.
An fi yi masa raga-raga, inda aka nuno shi Edochie din rike da kwalbar barasa, ya yi shigar malaman Musulunci.
Hatta Kiristoci masu dimbin yawa sun ragargaji Edochie, tare da cewa ko a nan kadai ya isa ya bata wa Musulmi rai.