Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya yi barazanar maka Daily Trust kotu, tare da neman diyyar naira bilyan 6, saboda abin da ya kira bata masa suna da ya ce jaridar ta yi.
Sannan kuma zai hada da wani marubuci mai suna Iliyasu Gadu dangane da batuncin da ya ce Gadu ya yi masa a cikin jaridar.
Zazzafan rubutun da ya harzuka Fani-Kayode ya biyo bayan tozarta wakilin jaridar mai suna Charles Eyo a Calabar kwanan baya.
Tsohon ministan ya rika surfa wa dan jaridar zagi, don kawai ya nemi jin ko akwai wanda ke daukar nauyin rangadin jihohi da Fani-Kayode ke yi.
Wani bidiyon arangamar da Fani Kayode ya yi da wani dan jarida, ya nuna cewa wulakancin da ya yi wa Eyo, cikin cokali ne.
Sai dai kuma bayan ya sha caccaka, daga baya Femi Fani-Kayode ya bada hakuri tare da janye kalmar mutumin banza da ya kira Eyo da ita.
Sai dai kuma a wani ra’ayi da na Iliyasu Gadu da Trust ta buga a narar Lahadi, ya kira Fani-Kayode “Dan Kwaya A Cikin Sufurar Karimci.” Wato da Turance, “Drug Added Thug in Designer Wears.”
Gadu ya yi wa Fani-Kayode wankin babban bargo a cikin rubutun.
Raddin Fani-Kayode
Ya ce an ci mutuncin sa, kuma an kwance masa zani a kasuwa. Don haka ba zai hakura ba.
Lauyan sa ne ya rubuta wasika zuwa ga Trust da Gadu. Lauyan mai suna Adeola Adedipe, ya ce an zubar wa Femi Fani-Kayode mutunci a jihar sa ta asali da kuma kasar sa.
Lauya ya nemi Trust ta bada hakuri a cikin kwana 14, ta buga a manyan jaridu biyu, kuma ta biya shi diyyar bata suna har naira bilyan 6.
Ya ce idan kamfanin Daily Trust ya ki yin haka, to zai maka shi kotu.