Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana alhinin ta kan lamarin nan na fashewar tankar daukar man fetur wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 20 a unguwar Felele da ke Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.
Ministar ta ce irin wannan abu ya na ta dada faruwa, kuma abin damuwa ne matuka, saboda an sha samun fashewar motar daukar fetur ko iskar gas a sassan kasar nan a cikin ‘yan watannin nan.
Ta ce: “Na tausaya kwarai kuma na damu da aukuwar wannan abu wanda ya ci rayukan mutane da dama waɗanda ba su ji ba ba su gani ba. Ina yi wa iyalan su da gwamnati da al’ummar Jihar Kogi ta’aziyya a kan faruwar wannan abu. Ina kuma addu’ar samun sauki cikin sauri ga wadanda su ka ji rauni tare da addu’ar Allah ya jiƙan wadanda su ka rasu.”
Mai ba ministar shawara kan watsa labarai, Nnneka Ikem Anibeze, ta ce Hajiya Sadiya Umar Farouq ta yi kira da a yi bincike mai zurfi kan wannan abu da ya faru, kuma ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki tsauraran matakan kiyaye hadurra a kan hanyoyi da kuma kare matafiya.
Hukumar Kiyaye Hadurra a kan Hanyoyi (FRSC) a jihar ta ruwaito cewa mutum 23 ne su ka mutu, ciki har da wani magidanci da matar sa da ‘ya’yan su guda uku, da wasu dalibai biyar na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi da kuma ‘yan makaranta. Motoci 10 su ka salwanta a gobarar.
Rahotanni sun ce mutum 10 sun kone kurmus ta yadda ba za a iya gane su ba yayin da wasu mutum shida su ka samu kuna mai ɗan sauƙi.
Fashewar man ta faru ne lokacin da wata mota ƙirar tankar daukar fetur ta kwace ta auka wa wata mota safa mai ɗauke da fasinjoji a unguwar Felele.