Fadar shugaban Ƙasa ta maida wa Obasanjo Martani, tace shine ‘Gogarman Mai Raba Kan Ƴan Najeriya’

0

Fadar shugaban ƙasa ta maida wa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo martani cewa shine yanzu ‘Gogarman mai raba kan Ƴan Najeriya.’

A doguwar martani da kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya saka wa hannu ranar Lahadi, ta ce maimakon Obasanjo ya koma ya zama dattijon arziki mai haɗa kan ƴan Najeriya yanzu ya koma sai watangaririya yake yi kamar ba dattijo ba yana kokarin raba kan ƴan Najeriya.

Idan ba a manta ba, Obasanjo ya bayyana cewa a halin da Najeriya ke ciki yanzu kiris ya rage gabadaya komai ya daburce a kasar.

Ya ce a halin yanzu Najeriya na gab da zama hedikwatar kasashen da ke fama da tsananin talauci yunwa. Baya ga tsananin rashin tsaro da ake fama da shi ga kuma tsadar abinci da bai taba ganin irin shi ba.

“A yau Najeriya ta gaza a fannoni da dama, babu wani tasiri sai karin rarrabuwar kawuna da fatara da yunwa. Ta hanyar tattalin arziki kuwa, Najeriya ta zama cibiya da Hedikwatar yunwa, fatara da talauci ta duniya.

“Mu na ta ci gaba da taka tsani mu na hawa kololuwar lalacewa yadda kasashen duniya ke hango mu daga nesa a matsayin kasar da babu tsaro, kuma babu alamar sa.

“Kuma duk ba wani abu ne ya haddasa mana wannan jangwangwama ba, sai kwasar-karan-mahaukaciya da wannan gwamnati ke yi wa tsarin shugabanci da jagoranci.”

Sai dai kuma fadar shugaban kasa ta ce Buhari ya taka rawar gani a Najeriya.

” Buhari ya gyara kawance da ke tsakanin Najeriya da wasu kasashe da a baya kawance da kasar ya tabarbare. Kasashen sun hada da kasar Amurka, Saudiya, Rasha, da sauran su.

Masu yin fashin baki sun shawarci Obasanjo da ya koma ya zama dattijon arziki mai gyara kasa ba mai kawo rudani da rarrabuwar kai ba.

” Kila abinda ke bata masa rai shine ganin yadda wasu nasaraori da Buhari ya samu musamman na hadin kai da ya samu da majalisa da yayi nasarar baiwa majalisar jihohi da kotuna cin gashin kansu wanda gwamnatin sa ta PDP ta gaza yin haka.

Share.

game da Author