Duk jirgin saman da ya karya dokar Korona, za mu janye lasisin sa – Hukumar NCAA

0

Hukumar jiragen sama ta Kasa, NCAA ta gargadi kamfanonin jiragen sama da ke tashi da sauka a Najeriya cewa muddun basu kiyaye dokokin da aka saka don kare mutane daga kamuwa da yada Korona, za ta kwace lasisin wannan jirgi.

Babban Darektan Hukumar NCAA Musa Nuhu, ya shaida haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai a Legas.

Nuhu ya ce duk jirgin da aka sake samu bai kiyaye wadannan dokoki ba, zai fuskanci fushin hukumar NCAA din.

” Daga yanzu ba za mu lamunta wa duk jirgin saman da bai kiyaye dokokin Korona ba. Idan muka samu jirgi ya karya dokar, zamu janye lasisin sa sannan mu ci shi tara.”

Share.

game da Author