Tsohon mataikamin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya aika wa majalisar Dattawa wasika, inda ya yi kira ga majalisar ta hana duk wani bashi da za karbo shi daga waje don yin aikin da ba kudaden shiga zai samar wa Najeriya ba.
Atiku ya aika wa shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan da wannan wasika ranar Talata, yana rokon majalisar Dokoki ta Kasa ta hana duk wani bashi da za ciwo don yin aikin da ba kudin shiga zai rika samarwa kasa ba.
Atiku ya ce bai kamata ‘yan majalisa su zura ido Najeriya na neman fadawa cikin tsananin ambaliyar bashin da babu gaira babu dalili kuma su rika amincewa da haka.
” A shekarar 2015, ana bin Najeriya bashin Naira Tiriliyan 12, amma kuma zuwa Agustan 2020, bashin ya ninka har zuwa Naira Tiriliyan 28.
Bashin da ake bin Najeriya kuwa daga waje na neman zarce Dala biliyan 30. Sannan kuma abinda ake yi da su ba kudaden shiga ne suke samar wa Najeriya ba.
Atiku ya kara da cewa majalisar ta rika hana jihohi da ke neman ciwo bashi domin yin ayyukan da zai samar wa jihohin kudaden shiga ba.
Idan ba a manta ba majalisar Dokoki ta kasa ta amincewa shugaba Buhari ciwo ranta-rantaman bashi har sau uku daga waje.
Discussion about this post