Shugaba Muhammdu Buhari ya gana da hamshakin limamin Cocin RCCG, Enoch Adebayo, a tsakiyar lokacin da manyan limaman Kiristoci ke bijire wa sabuwar dokar da gwamnati ta kafa domin kula da asusun kudaden kungiyoyin da ba na kasuwanci ba, ciki kuwa har da coci-coci.
Wannan doka ta tayar da kura musamman a da’irar fasto-fasto na coci-cocin busharar zamani.
Yayin da Buhari ya gana da Adebayo, sauran wadanda ke wurin har da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, wanda shi ma fasto ne a Cocin RCCG karkashin Adebayo din.
Ba a dai ji batutuwan da suka tattauna ba, amma dai ana rade-radin cewa ganawar ba ta rasa nasaba da rudanin da ya taso a kan Dokar CAMA, wadda Buhari ya sa wa hannu kwanan nan.
Fasto David Oyedepo da Johnson Sulaiman duk sun tsine wa dokar, sun ce ba za su bi ta ba.
Ita ma Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta bayyana cewa “Dokar CAMA dokar Shaidan ce”, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ruwaito.
Kungiyar cewa ta yi “Dokar CAMA dokar Shaidan ce, CAN ba za ta amince da ita ba”, kamar yadda ta yi kurari a cikin wani gargadin Kungiyar Kiristoci ga Gwamnati.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bayyana cewa sabuwar dokar maida kamfanoni da kungiyoyi karkashin kulawa da sa-idon gwamnati ta ‘Company and Allied Matters Act’ (CAMA), dokar Shaidan ce da kuma shaidanci.
Akan haka CAN ta ce za ta bijire wa dokar, ba za ta bi ba.
Shugaba Muhammdu Buhari ne ya sa wa dokar hannu a ranar 7 Ga Agusta. Dokar ta tilasta wa kamfanoni da kungiyoyin addinai yin rajista da CAC kuma za su kasance a karkashin sa-idon wani Minista.
Har ila yau, dokar ya dai ta karfafa cewa gwamnati na da ikon cire shugabanni kwamitin amintattun wata Kungiyar addini idan akwai rikici ko tankiya a cikin shugabancin kungiyar.
A na ta raddin, Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta ce wannan doka karfa-karfa ce, ba abin yarda ba ce, kuma shaidanci ne, sannan kuma dokar yi wa Ubangiji shisshigi ce.
Kakakin Yada Labarai na CAN, Adebayo Olajide ne ya sa wa takardar sanarwar manema labarai hannu, wadda ta kunshi wadannan bayanai da kungiyar ta fitar.
CAN ya kara da cewa kungiyar addini na gudanar da hidimar daukaka kalmar Ubangiji da kudaden ta, tare da ayyukan kusantuwa ga Allah abin bauta.
Ya ce saboda haka, tunda dai addini na Ubangiji ne, ba gwamnati ake bauta wa ba, babu yadda za a yi Kungiyar CAN ta zauna karkashin kulawa ko sa-idon gwamnatin tarayya.
CAN ta gargadi gwamnati tare da jan hankalin ta cewa wannan doka kuskure ne babba gwamnati ta tafka, domin za ta iya zama hasken wutar fitinar da idan ta barke gwamnati ba ta da ruwan kashe ta, maimakon ta zama hasken zaman lafiya da lumana.
CAN ta shawarci gwamnati ta maida hankali wajen samar wa al’mma ayyukan jin dadin rayuwa da samar wa jama’a dawwamammen zaman lafiya.
Discussion about this post