Dattijon da ke tsoron mutuwa a shekaru 70, ya binciki imanin sa – Fasto Adebayo

0

Limamin Babban Cocin RCCG, Enoch Adebayo, ya ce duk dattijon da ya kai shekaru 70 har ya haura, kuma ya ke tsoron mutuwa, to ya binciki imanin sa.

Adebayo ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi, lokacin taron godiya ga Ubangiji a Hedikwatar cocin na sa da ke Lagos.

“Saboda tsoron kamuwa da cutar Korona, an ce wa dattawa duk su zauna a gida su daina fita.

“To amma duk dattijon da ya haura shekaru 70 a duniya, kuma a haka ya na tsoron mutuwa, to ya binciki imanin sa.”

Daga nan ya ci gaba da cewa su fito kawai, ita cutar Coronavirus ba ta illata wanda ya yi amanna da Ugangiji.

“Mu ci gaba da godiya ga Ubangiji, sai ya kare mu a kan duk wani bala’i. Tsararrakin haihuwar mu idan ku ka duba, wasu sun mutu, wasu na kulle a kurkuku, wasu na kwance asibitii. Wannan kaɗai ya isa kai da ke raye, Kuma cikin koshin lafiya ka gode wa Ubangiji.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda wani fasto ya ce zai iya rungumar mai dauke da cutar Korona ya yi masa addu’a, kuma babu abin da zai same shi.

Sannan kuma ta buga labarin Shugaban Kungiyar CAN reshen Jihar Adamawa, Bishop Mamza na cewa ana zuzuta cutar Coronavirus da ya yawa. Kuma hakan ke firgita mutane su na mutuwa.

Ya ce yawancin mutane da an ce su na dauke da cutar Coronavirus, to sai su firgita, su kasa barci, su ga kamar umarnin tafiya lahira ne aka ba su.

Korona na ci gaba da illa, ko da ya ke dai ta dan fara lafawa, har a gwamnatin tarayya ta aza ranar sake bude makarantu baki daya.

A labarin, PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin cewa masu firgita mutane ke kashe masu cutar Korona, inji Shugaban CAN bayan ya warke.

Share.

game da Author