Sabon bayanan kididdigar da NEITI ta fitar a ranar Talata ya nuna Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi sun raba wa junan su jimillar naira tiriliyan 3.88 a cikin watanni shida.
Watannin da aka raba kuɗaɗen sun kama ne daga Janairu 2020 zuwa Yuni 2020.
Bayanan kididdigar wanda aka fitar a Abuja, ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta kwashi naira tiriliyan 1.53, ta bai wa jihohi naira tiriliyan 1.29. Su kuma Kananan Hukumomi 774 aka raba musu naira bilyan 771 a cikin watanni 6.
Kididdigar ta nuna cewa naira tiriliyan 1.53 da Gwamnatin Tarayya ta samu tsakanin Janairu zuwa Yunin 2020, ba su kai yawan waɗanda ta samu daga Janairu zuwa Yunin 2019 ba. A wancan shekara naira tiriliyan 1.599 ta samu.
Haka kuma kudin da Gwamnatin Tarayya ta samu tsakanin Janairu zuwa Yunin 2018, sun zarce wanda ta samu a bana. A 2018 ta karbi naira tiriliyan 1.652 tsakanin Janairu zuwa Yuni.
Raguwar Samun Kuɗaɗen Shiga:
Kuɗaɗen shigar da Gwamnatin Tarayya ke samu sun ragu domin naira tiriliyan 1.62 kaɗai aka tara tsakanin Janairu zuwa Mayu na 2020.
Wannan adadi kuwa ya nuna an samu gagarimin gibi har na kashi 38% kenan, domin ita Gwamnatin Tarayya ta yi kirdado da hasashen cewa naira tiriliyan 2.62 ta ke sa ran ta tara tsakanin Janairu zuwa Mayu din wannan shekara.
Waɗanne Jihohi Aka Fi Sheka Wa Ruwan Kuɗi?
Jihar Delta ce aka fi gabza wa madarar ruwan kudi a cikin watanni 6, har naira bilyan 100.81.
Wace Jiha Aka Fi Bai Wa Kuɗi Cikin Cokali?
Jihar Osun ce ta fi karɓar kuɗi mafi ƙaranci a tafin hannu, domin naira bilyan 13.13 kacal ta karba a cikin watannin Janairu zuwa Yuni.
Kenan Jihar Delta ta nunka Osun karɓar maƙudan kuɗaɗe, har sau nunki 7.
Kwatankwacin Yawan Kuɗaɗen Da Delta Ta Karba:
Naira bilyan 100.81 da Delta ta karɓar ita kadai, ya zarce kudaden da jihohin Osun, Cross River, Filato, Ogun, Gombe da Ekiti suka karba.
Wadannan jihohi su 6, sun karbi jimillar naira bilyan 99.47 a cikin watanni 6.
Jihohi 4 Da Aka Fi Zabga Wa Kuɗaɗe:
Wadannan jihohi 4, wsto Delta, Rivers, Akwa Ibom da Bayelsa, sun karbi naira bilyan 321.29. Abin da wadannan jihohi 4 suka karba ya zarce naira bilyan 314.08 da jihohin Osun, Cross River, Filsto, Ogun, Gombe, Ekiti, Zamfara, Kwara, Nasarawa, Ebonyi, Taraba, Benuwai, Adamawa, Ondo, Bauchi da Abia suka karba.
Jihar Lagos ce aka fi yankar wa ƙudade, sai kuma Jihar Yobe aka fi yankar wa adadi mafi ƙanƙanta.