Ministan Ma’aikatar Jinkai Sadiya Farouq ta bayyana cewa daga yanzu za a riƙa jefawa ƴan gudun hijra abincin tallafi daga saman jirgi.
Sadiya ta ce dalilin yin haka kuwa shine domin kaucewa hare haren Boko Haram, rashin hanyar mota zuwa wasu daga cikin sansanonin ƴan gudun hijran da kuma lokaci yanzu na damuna da wasu wuraren ba su shiga saboda ruwa da ambaliya.
Tuni dai har ministan ta gana da jami’an sojojin sama wanda da jiragen su za riƙa yin wannan aiki a jihar.
Kwamanda Precious Amadi, na rundunar sojin saman Najeriya, wanda shine zai jagoranci wannan aiki ya yabawa wannan tsari na ma’aikatar Jinkai yana mai cewa hakan yayi daidai kuma ba za a samu matsala ba.
Bayan ganawa da tawagar ma’aikatan tsaron sama da minista Sadiya ta yi ta ta kuma gana da gwamnan jihar Barno Babagana Zulum a fadar gwamnati dake Maiduguri.
Za a raba wa ƴan gudun hijira, Shinkafa, Masara, Dawa, Mangyada, Manja, da sauran su.