Dalilin da ya sa muka rusa gidajen karuwai da mashaya a Sabongari – Usman

0

Shugaban karamar hukumar Sabongari dake jihar Kaduna Mohammad Usman ya bayyana cewa rufe gidajen Karuwai da mashaya barasa a karamar hukumar ya kawo raguwar ta’addanci a ƙaramar hukumar.

A tattaunawa da yayi da manema labarai a Zariya, Usman ya ce wasu gidajen giyan da karamar hukumar ta rusa basu da lasisin bude shago irin haka a jihar.

” Tun bayan rusa irin waɗannan wurare mutanen Sabongari suka riƙa bin mu da addu’oi na alkhairi saboda wannan abu da muka yi, suna cewa dama wuraren suna lalata musu tarbiyyar ƴaƴa.

” Ko da muka nemi masu gidajen giya su zo su sabonta takardun su na bude wurare irin haka, da yake kashi 90 bisa 100 daga cikin su basu da lasisi, sai suka ki zuwa.

” Sai bayan mun rusa sai suka kai mu kotu. A kotun ma mun yi nasara a kan su.

Share.

game da Author