Dalilin da ya sa Buhari ya cire tallafin man fetur da na wutar lantarki – Fadar shugaban Ƙasa

0

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana wasu dalilai da ya sa shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya cire tallafin man fetur da na wutan lantarki da talakawa ke ta ƙorafi akai.

A wata takarda da aka fitar daga fadar shugaba Buhari wanda kakakin fadar Garba Shehu ya saka wa hannu, Shehu ya shaida cewa Buhari yayi haka ne domin ya kau da rashawa da yayi wa tsarin katutu sannan da kuma daƙile watanda da ake yi da kuɗin talakawa a dalilin wai ana biyan tallafi.

” Tun bayan ɗarewa kujerar mulki da APC ta yi a 2015, gwamnatin Buhari ke kokarin kawo sauyi a fannonin man fetur, Wutan Lantarki da Taki. Gwamnati ta sakar wa ƴan kasuwa su riƙa siya su na saida abin su domin a kauce wa rashawa da handama da wasu ke yi.

” Ina so mutane su tuna cewa baya ga matsalar da annobar Korona ta jefa kasa da yayi sanadiyyar taɓarɓarewar arzikin ƙasa, gwamnati na fama da hare haren Boko Haram har yanzu, sannan kuma Ambaliyar ruwa a wasu yankunan ƙasar nan, ga kuma rashin samun isassun kuɗaɗen shiga da kuma hare haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane, duk waɗannan sune gwamnati ke fama da su.

” Amma ina tabbatar muku cewa tarihi zai wanke Buhari ta-tas cewa baya ga zama shugaban Ƙasan da yafi kowa yawan jama’a da da masoya, za a tuna dashi cewa shine shugaban da yayi fito na fito da cin hanci da rashawa a kasar nan da bunkasa tattalin arzikin ƙasar domin cigaban ta.

A ƙarshe Shehu ya yi kira ga ƙungiyoyi na kwadago da na kare hakkin Ɗan Adam da su fahimci shugaba Buhari su cigaba da mara masa da bashi goyon baya a ayyukan cigaban kasa da ya sa a gaba.

Share.

game da Author