Karamin Minsiatan Harkokin Man Fetur, Timipre Sylva, ya jaddada cewa ba Gwamnatin Tarayya ce ke yanka farashin da ake sayar da litar man fetur a kasar nan ba.
Sylva ya bayyana wa manema labarai haka dangane da haushi da damuwar da dimbin ‘yan Najeriya ke ci gaba da nunawa a kan karin kudin litar man fetur da aka yi.
Farkon makon nan ne Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur ta maida litar fetur farashin sari ga ‘yan kasuwa kan Naira 151. Su kuma dillalan suka kara naira 10 ladar jigilar kowace lita, inda suke sayar da lita daya naira 161.
Sylva ya ce abin takaici ne ganin yadda jamai ke dora wa Gwamnatin Buhari laifi.
Ya ce har yanzu muradin wannan gwamnati shi ne ta samar da saukin rayuwa ga al’ummar Najeriya.
“Kun dai san Shugaba Muhammadu Buhari shi ne gadon bayan goyon marayu, musamman talakawan Najeriya.” Inji Sylva.
“Babu yadda za a yi haka kawai Buhari ya goyi bayan a kara farashin fetur, har sai fa idan tura ta kai bango, ya ga babu wata mafita idan ba a yi karin ba.
“Kun kuma ga yadda cutar Coronavirus ta karyar da farashin fetur ya koma kamar farashin ruwan aski.” Inji Sylva.
Ya ce karin ya zama dole, saboda gwamnati ba ta iya biyan kudaden tallafin man fetur.
Sai dai kuma yayin da kowa ke kokawa wannan karin kudin fetur da na wutar lantarki, jam’iyyar APC cewa ta yi Gwamnatin Buhari ta kara kudin fetur da wutar lantarki don ‘yan Najeriya su ji dadi.
Jam’iyyar APC ta ce Gwamnatin Tarayya ta kara farashin wutar lantarki da na man fetur domin jin dadin ‘yan Najeriya.
Wannan bayani ya fito ne a matsayin raddi ga jam’iyyar PDP, wadda a ranar Laraba ta shiga sahun ‘yan Najeriya masu sukar karin farashin fetur da na hasken lantarki.
Cikin sanarwar da PDP ta fitar a ranar Labara bayan gwamnati ta fito da sabon farashin sarin litar fetur naira 151 daga NNPC, jam’iyyar PDP ta ce ba ta yarda da karin ba.
“Kun ce a kori PDP saboda a gwamnatin ta ana saida fetur naira 87. To ga shi nan a karkashin APC, tun ba a je ko’ina ba lita daya ta koma naira 161.” Inji PDP, cikin sanarwar da Kakakin Yada Labarai Kola Olagbondiyan ya fitar.
Gwamnatin Buhari ta kara kudin fetur kwanaki biyu bayan nunka kudin wutar lantarki daga naira 30.36 mitar wuta daya, zuwa naira 66 mita daya.
A na ta martanin, jam’iyyar APC ta ce an yi wannan kari ne saboda lalubo hanyoyin da ‘yan Najeriya za su samu saukin rayuwa.
A sanarwar da Mataimakin Sakataren Yada Labarai, Yekini Nabena ya fitar, APC ta ce duk wannan galauniya da ake fama da ita, ta samo asali ne daga matsalar da mulkin PDP na shekara 16 ya jefa Najeriya.
“Rashin kunya ce da PDP ta fito ta na sukar karin farashin fetur. Domin ita ce silar shigar Najeriya cikin wannan matsalar. Me zai hana su dawo da kudaden tallafin man fetur din da suka danne a tsawon shekaru 16 su na mulki.”
Tuni dai wannan kari ya haifar da maganganu, har mutane da dama na tuna mulkin Jonathan.
Karin farashin fetur da na wutar lantarki, ya zo a daidai lokacin da tsadar kayan abinci na neman abincin ya gagari talaka a Najeriya.