BUKIN AUREN HANAN: Yadda Buhari da iyalan sa suka karya dokar Babban Bankin Najeriya da dokar Korona

0

Ƴan Najeriya sun dira wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da iyalan sa inda suka rika caccakar su bisa kararraya dokinkin kasa wajen bukin ƴar su Hanan Muhammadu Buhari.

Idan ba a manta ba an yi bukin Aisha Buhari wanda ake kira da Hanan, da Turad Sha’aban ɗan tsohon ɗan majalisar Tarayya ne daga jihar Kaduna ranar Juma’ar da ta wuce.

Irin abubuwan da ƴan Najeriya suka gani a wurin taron bukin cikin hotuna da bidiyo wanda wasu daga ciki uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da kanta ta saka su yayi matukar daure musu kai da saka su cikin rudani ganin yadda iyalan shugaban suka ragargaza dokokin kasa a lokacin bukin.

Da farko dai dokar Babban Banki Ƙasa da ke ƙunshe a ƙundin tsarin Mulki ya hana wulaƙanta kuɗin ƙasa.

Wulaƙanta kuɗin ƙasa kuwa kamar yadda dokar take ya haɗa da yin liki a wajen buki sannan ana tattaka kuɗin gangar.

A wannan buki kuwa an nuna yadda Hanan da mijinta Turad suka riƙa cashewa ana lika musu sabbin nairori suna buga rangwada mai waka kuma yana ta nuna kwazon sa.

Kamar yadda doka ta zo da shi duk wanda yayi haka wato ya wulaƙanta kuɗin ƙasa za aci shi taran naira 50,000 ko kuma yayi zaman gidan kaso na wata shida. Dokar ta haɗa da yaga kudi, liki a biki ko taro, taka kudi, buga wa kudi tambari da dai sauran abin da zai latata kudi.

Haka kuma dokar Korona da aka saka a kasa ya hana gwamatsuwar mutane a wuri ɗaya, sannan kuma dokar ta umarci mutane su riƙa saka takunkumin fuska a duk lokacin da za su taru.

An gani a Najeriya yadda aka tsare wasu domin karya wannan doka, aka gurfanar dasu a kotu.

A wannan buki na Hanan, an nuna amarya da angonda abokai da kawaye na taka rawa son ran su a cakude da juna babu takunkumin fuska a cikin su.

Kakakin fadar shugaban Ƙasa, Garba Shehu bai amsa kiran waya da akayi masa ba haka kuma shima kakakin babban bankin Kasa Isaac Okoroafor, shima bai amsa waya ba.

Share.

game da Author