Buhari ya umarci ministoci su riƙa yayata ayyukan da gwamnatin sa ta yi wa jama’a

0

Shugaba Muhammdu Buhari ya yi kira ga ministocin sa su maida hankali sosai wajen yayata irin ayyukan raya ƙasa da raya al’umma da gwamnatin sa ta samar.

Ya ce su maida hankali sosai kada su yi sanyin jiki har masu adawa da waɗanda ba su fatan alheri a gwamnatin sa su riƙa watsa surutan da za su dusashe hasken tauraron gwamnatin sa.

Buhari wanda ya ce ya na nan ya na ƙoƙarin cika muradin sa na ganin ya ceto mutum milyan 100 daga fatara da talauci. Ya kuma ce ko masu hassada sun san cewa gwamnatin sa ta yi rawar gani a cikin wannan shekara daya.

Buhari ya yi wannan bayani ne daidai lokacin da rashin aikin yi ke kara dumfarar ƴan Najeriya da dama, ƙarin kuɗin fetur, ƙarin kuɗin wutar lantarki da kuma hauhawar farashin abincin da talakawa ke yi, wanda a yanzu ke neman ya gagare su.

Wannan bayani Buhari ya yi shi a wurin rufe taron Sanin-makamar-aiki da aka shirya wa Ministoci, Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da sauran manyan jami’an gwamnati.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha a faɗa a ranar bude taron cewa, “shekarar farko ta zangon Buhari na biyu, ita ce mafi ƙarsashi fiye da sauran shekarun baya da ya shafe a kan mulki.”

A ranar Talata Buhari ya ce, “ayyukan da ministoci suka yi ya nuna cewa an matsa gaba sosai da tafiya mai nisa, ba a wuri guda ake ta tuma tsalle ba. Duk kuwa da dimbin kalubalen da aka rika cin karo da su.” Inji Buhari.

“Bari kuma na kara jaddada cewa wannan gwamnati ta na nan a kan bakan ta na tabbatar da ta ceto ‘yan Najeriya milyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.

Buhari ya ci gaba da wasa kan sa da kan sa, ya rika bayyana nasarorin da ya ce ya samu kamar gina titin jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan. Sai ci gaba da aikin da jiragen kasa ke yi kaga Abuja zuwa Kaduna. Ya kuma ce a na kokarin a ga cewa an ci gaba da aikin titin jiragen na kasa daga Ibadan zuwa Kano da kuma na Fatakwal zuwa Maiduguri.

Ya ce ya na sa ran kamalai gadar Kogin Neja nan da shekarar 2023. Buhari ya jinjina wa gwamnatin sa wajen bangaren samar da tsaro da wasu bangarori masu dama da ya yi bayani a kai.

“Ina umartar ku da kowa ya zare makaman kare gwamnatin nan ta hanyar yayata ayyukan alherin da muka yi wa jama’a. Kada ku bari wasu sakarkaru da masu makauniyar adawar siyasa su ci gaba da watsa karairayi a kan wannan gwamnati.” Inji Buhari.

Share.

game da Author