Buhari ya ƙara gargaɗin CBN kada ya kuskura ya bada lasisin shigo da abinci da takin zamani

0

Shugaba Muhammdu Buhari ya kara jaddada gargaɗi ga Babban Bankin Najeriya (CBN) cewa kada bankin ya sake ya kara bayar da musayar kudaden waje ga masu shigo da abinci da takin zamani daga kasashen waje.

Cikin 2019 ma PREMIUM TIMES ta buga labarin irin wannan gargaɗi da Buhari ya yi wa CBN.

Buhari ya yi wannan gargaɗi ne yayin ganawa da Majalisar Wadata Kasa da Abinci, a ranar Alhamis a Fadar Shugaban Kasa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Buhari, Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya bayar da wannan kakkausan umarni ne cewa, “Kada CBN ya kuskura ya kara bayar da canjin kudaden waje ko na sisin-kwabo, domin shigo da abinci da takin zamani daga kasashen waje.”

Ya ce idan aka bari aka ci gaba da shigo da abinci da takin zamani daga waje, to hakan zai kashe tasirin manoman cikin gida kenan.

“Duk mai bukatar shigo da abinci daga kasar waje, ya je duk inda zai samo canjin kudi ya samo, ya je ya sayo. Amma dai kada CBN ya kuskura ya bada canjin kudi ga masu shigo da abinci da takin zamani.

“Mu na da matasa karti majiya karfi da ke shirye domin bada himma su yi aiki. To ga noma nan, duk maji-karfi ya je ya yi, shi ne mafita. Mu kuma mu na da gagarimin shirin tallafa wa manoma.” Inji Shugaba Buhari.

Shugaba Buhari ne Shugaban Kwamiti, sauran da suka halarci taron sun hada da Mataimakin Shugaban Kwamiti, kuma Gwaman Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari, sai kuma gwamna daya da ke wakiltar kowace shiyya daga Shiyyoyi Shida na kasar nan.

Gwamnonin sun hada na da Jigawa, Filato, Taraba, Ebonyi, Lagos da Kebbi.

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ta yi bayanin irin hanyoyin da gwamnatin tarayya ta bijiro da su wajen dakile kalubalen da kasar nan ta fuskanta sanadiyyar barkewar cutar Korona.

Share.

game da Author