Birtaniya ta maida wa Najeriya dala 100,000, kudin da aka damfari wani dan Najeriya

0

Birtaniya ta maida wa Najeriya dala 100,000, wasu kudi jami’an tsaro su ka kwace a hannun wani dan kasuwa mutumin Najeriya, mai suna Nasiru Danu, bayan da kotu ta wanke shi daga aikata laifi.

Takardun kotu da kuma takardun bayanan banki wadanda PREMIUM TIMES ta gani, sun nuna cewa an biya kudin tare da kudin ruwan da uwar kudin ta haifar tsawon shekara daya, kamar yadda wata Kotun Majistare ta bayar da umarni a ranar 7 Ga Satumba.

Jami’an Tsaron Kan Iyakoki da Jami’an Shige-da-fice na London ne su ka rike Danu a filin saukar London, a ranar 13 Ga Satumba, 2019.

An tsare shi ne bayan sun gano cewa ya na dauke da fasfo na shiga Ingila na jabu.

PREMIUM TIMES ta gano cewa wani kamfanin zirga-zirga ne ya damfari Danu, inda ya karbi dala 35,000 daga hannun sa, da sunan zai samo masa fasfo.

A rashin sani, Danu ya karbi fasfo wanda jabu ne daga hannun kamfanin zirga-zirgar.

Bayan ya dawo Najeriya, Danu ya rubuta takardun korafi zuwa Ofishin DSS, inda ya bada rahoton damfarar sa kudi da aka yi, ya biya fasfo na jabu a rashin sani.

Daga nan SSS su ka maida maganar a hannun EFCC, su kuma su na ta tuhuma da binciken wani mai suna Rabbi Okpara.

Cikin Disamba 2019, PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda EFCC ta gurfanar da Okpara a Babbar Kotun Tarayya, bisa zargin damfarar Danu wasu kudade shi da wasu ‘yan Najeriya.

Okpara shi ne mai kamfanin zirga-zirgar fita waje, mai suna Green Valley Concept Limited.

Lauyoyin Danu sun garzaya kotu neman Ingila ta sakar masa kudin sa, kuma tuni kudin sun shiga asusun bankin sa.

Share.

game da Author