BINCIKEN MUSAMMAN: Yadda PREMIUM TIMES ta karade Kudancin Kaduna, ta gano kashe-kashen ramuwar-gayya ke hana yankin zaman lafiya

0

‘Katilan-makatulan’: Ranar 18 Ga Agusta,2020, a kauyen Unguwan Garkon, mahara sun ritsa Hanatu Kefas da ‘yar ta mai shekara uku. Aka ce ta balle ganin goyo ta ajiye yarinyar a gefe. A tunanin ta fyade za a yi mata. Amma sai maharan wadanda aka hakkake Fulani ne, su ka rufe ta cikin garken aladu, aka yi ta yi tsirara ta rika birgima cikin dagwalon kazantar dagwallatsin kazantar kashin adalun nan.

Hanatu Kefas ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa haka ta rika birgima ta na damalmala wa jikin ta kashin alade. Ta na cikin haka ta rika jin ana dankara wa mijin ta harbi da bindiga.

“Ina ji ina ganin sa ya na kakarin mutuwa, amma ba ni da ikon matsawa kusa da shi.”

Kisan da aka yi wa mijin ta Maliki Kefas, ya gigita ta, har sai da aka kwantar da ita asibitin Zonkwa, cikin Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.

“Ramuwar Gayya Fulani Su Ka Yi A Kauyen Mu” – Hanatu Kefas

Bayan kisan da aka yi wa mijin Hanatu, an kashe wasu mutane uku. Maharan, wadanda Fulani ne, “sun zo ramuwar gayya ne a Unguwan Garkon, saboda a baya an kashe wani dan uwan su Bafulatani. Amma dai ni ban san wadanda su ka yi kisan ba. Saboda na je Kaduna, na dawo na taras an yi kisan.” Inji Hanatu, a hirar da PREMIUM TIMES.

A wannan harin ramuwar-gayya da Fulani su ka kai, ba su taba mata ba. Maza kadai su ka rika farauta, kuma sun kashe mutum biyu bayan mijin Hanatu.

Wannan hari alama ta irin salo da musabbabi da kuma dalilan da ke sa kashe-kashen zubar da jinainai a Kudancin Kaduna ya ki ci, ya ki cinyewa.

“Tasirin Kabilanci Da Asalanci A Kashe-kashen Kudancin Kaduna”:

Kudancin Kaduna mai ƙabilu daban-daban wadanda mafi yawan su Kiristoci ne, akwai kabilu irin su Kataf, Kaje, Adara, Takad, Fantswam, Ikulu, Chawai, Ham, wadanda su ne mafi yawan al’ummar yankin.

Sannan kuma akwai Hausawa da Fulani waɗanda su kuma Musulmi ne, amma su sauran ƙabilun yankin ba su yarda cewa Hausawa da Filani ‘yan asalin yankin ba ne.

Akwai tsirarun ƙabilu a yankin waɗanda ba Hausawa ba ne, ba kuma Fulani ba ne, amma kuma Musulmai ne. Su ne irin su tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Usman Mu’azu, musulmi ne dan kabilar Ham. Sai kuma irin su Mataimakiyar Gwamna Nasir El-Rufai, Hadiza Balarabe, ƴar ƙabilar Numana ce, kuma Musulma.

Su dai Hausawan yankin sun yi ikirarin cewa tun wajen shekarar 1650 su ke a yankin, su ne ma su ka kafa garin Zangon Kataf a shekarar.

Akwai Fulanin da ke shiga yankin su na kiwon shanu da damina, saboda yalwar ciyawa da yankin ke da shi. Amma dai sauran haifaffin Kudancin Kaduna wadanda Hausawa da Fulani ne, sun ki amincewa a ce musu su ba ‘yan asalin yankin ba ne.

Wani Kiriasta kuma shugaban yankin sa mai suna Gambo Waziri, cewa ya yi, “duk rigimar nan ta su wa ne ne ‘yan asali su wa ke bare ce. Mu ne ‘yan asali. Saboda ko da shekara 300 na yi a Enugu, ba za a kira ni dan asalin yankin kabilar Enugu ba.”

Kashe-kashen Kudancin Kaduna: Rikicin Gonaki, Addinanci, Kabilanci

“Kasar mu, ko kuma na ce maka gonakin mu daga kakannin- kakannin mu duk mu kagaje su.” Inji Saidu Umaru, wani dan kabilar Fantswam kuma jagora, Dagacin Zikfak ta Masarautar Kafanchan, cikin Karamar Hukumar Jema’a.

Wannan ra’ayi na sa ya yi daidai da ra’ayin duk wani kabila kirista dan yankin Kudancin Kaduna, ko ma a wace Karamar Hukuma ya ke a yankin.

Katutun Kiyayya, Gaba, Rashin Amintar Juna:

Wakilin mu ya fahimci a bangarorin biyu akwai tsananin gaba, kiyayya da rashin amintaka a duk inda ya shiga, tsawon kwanaki da ya shafe ya na karakaina a kananan hukumomin jihar.

Duk bangarorin da akan kai wa hari, akan lalata musu abin da suka fi takama da shi na dukiya, baya ga kisan rayuka. Duk bangaren da aka kai wa hari, sai sun rama komai daren dadewa.

Amma wakilin mu ya lura a yankin akwai hare-hare da ba su da alaka da rikice-rikicen ƙabilanci, wato irin na masu garkuwa da mutane da ke ritsawa da mai tsautsayi.

Manyan Kiristoci da wakilin mu ya yi hira da su, su na ganin kamar wasu tsare-tsaren da Gwamnatin Kaduna ta fito da su, duk na kokarin danne yankin ne. Amma akwai masu ganin cewa akwai bukatar a yi zaman kaunar juna tsakanin bangarorin biyu a yankin.

Shi ma babban Limamin Babban Masallacin Kafanchan, Muhammad Kassim, cewa ya yi sai bangarorin Kiristoci da Musulmi sun fahimci juna sun zauna lafiya sannan yankin zai samu kwanciyar hankali.

Duk Maganar Ɗaya Dai Ce

Ko a Iburu ko a Kajuru, ko a Kasuwan Magani ko a Kafanchan ko a Zangon Kataf ko ma ina a yankin Kudancin Kaduna har ka haɗa da kashe-kashen yankin ƙabilar Adara, duk dai magana ce ta rashin hakuri da juna, gaba, kiyayya, ƙabilanci, addinanci da kuma ramuwar-gayya.

Haka abjn ya ke a kashe-kashen da aka yi a Gidan Dutse, Kujeni da Bakira, duk na ramuwar-gayya ce.

PREMIUM TIMES ta gano wasu munanan hare-hare da aka har 11 a Gonan Rogo, Makyali, Ungwan Rana, Idazu, Ungwan Araha, Ungwan Dantata, Agwala Dutse, Tudu Doka Avong da Unguwan Magayaki da aka kashe akalla mutum 70.

PREMIUM TIMES ta mallaki sunayen wadanda aka kashen da kuma munanan raunukan da aka ji musu kafin a kashe su.

Hare-haren na ramuwar gayya kowane bangare kan yi asarar rayuka da dukiyoyi har ma da kone gidaje ko rugage.

An ce akwai akalla masu gudun hijira Katafawa 3,455 a wata makarantar Cocin ECWA da ke Zonkwa, Karamar Hukumar Zangon Kataf. Amma dai wakilin mu ya ce ya samu masu gudun hijira ba su fi 100 ba.

Wani jami’i ya ce akwai sansanin gudun hijira na Fulani a Kamoru, karkashin Zangon Kataf, inda Fulanin da aka tarwatsa wa rugage a Lisudu da kauyen Boto su ke can zaune.

Sai dai PREMIUM TIMES ta gano a sansanin Kamoru, an tsugunar da Fulani ne kamar 200, kuma ba su wuce kwana uku a wurin ba.

Wannan kashe-kashen da a yanzu haka Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin Gwamna Nasir El-Rufai na so ya kawo karshen sa, ya zama tarihi. Sai dai kuma Musulman yankin na ganin duk wani abu da za a yi to dole sai an koma wa Rahoton Kwamitin Bincike na Rikicin 1992, wanda aka kashe dubban Musulmai. Su kuma masu magana da yawun jama’ar yankin na cewa bimbinin wancan rahoto na baya ba zai haifar da da mai ido ba. Domin su su na ganin hari ne aka nemi a shafe su a bayan kasa, amma kuma su ka nuna jarumta su ka kare kan su.

Da alama babu ranar kare wannan rikice-rikice, domin PREMIUM TIMES na da munanan hotunan barnar da aka yi wa Fulani cikin watan Yuni, ranar 11 da 12 Ga wata, inda aka banka wa gidaje 36 wuta a kauyukan Gidan Zaki, Zarkwai, Takamaimen, Kigudu, Makwakwu, Bakin Kogi, Shilliam, Gidan Gata, Gidan Avong da Gora.

Ko ya kokarin da Gwamna El-Rufai ke yi na wanzar da zaman lafiya a Kaduna zai karke? Ko za a bari ya yi karko kuwa? Bari mu sa-ido mu gani.

Share.

game da Author