Abin mamaki da takaici shi ne, ace muna karni na ashirin da daya amma ana mana wakilci irin na mutanen da basu san me ya dace dasu ba! A daidai lokacin da duniya take cigaba da bunkasa ta fannin kimiya da fasaha amma ace wai a wannan lokacin ake dakushe mana tunani da yin wasa da hankulan mu a siyasance.
Yanzu lokaci ne da ake gina tunani da fasaha ta hanyar samar da ingantaccen ilimi ba neman suna ta kowane hali ba, alummar karamar hukuma ta sun fi bukatar a tallafa musu gurin samun ingantaccen ilimi domin samun damar da za a dama dasu a fadin duniya. Amma rashin sanin me alumma suke bukata ko kuma ince rashin iya wakilci yasa aka gudanar da taron tozarci da sunan bada tallafi, tallafin da ba zai inganta rayuwar mutane ba.
An karade kafafen yada labarai da karerayin za ayi taron bada jari ga alummar karamar hukumar fagge, wanda ba a taba yin kamar shi ba. Kwatsam sai gashi mun wayi gari da ganin injin markade da keken dinki tsohon yayi {tako-tako} a matsayin kayan da ake ikirarin zasu canjawa mutane rayuwa!

Dukkan abubuwan da aka raba abubuwa ne da aka daina yayin su ko ince lokacin su ya shude a duniya yar zamani, kwanakin baya wata yar majalisar tarraya ta garin Borno Dr. Zainab Gimba tayi gagarimin taron bada jari inda alummar da take wakilta suka rabauta da motoci, mashin mai kafa uku da injin ban ruwa na noma da makudan kudade duk dan ta canja rayuwar alummar ta. Amma gashi anyi mana yar burum-burum da sunan bada tallafi a karamar hukumar mu.
A namu tunanin mun dauka alummar karamar hukuma ta na da daraja da kimar da za a basu injinan zamani domin su bunkasa sanao’in su, ashe basu kai wannan matsayin ba har daren gobe a kaskance muke a gurin wanda muka samawa aikin yi a garin Abuja. Bangaren kekunan dinki na zamani akwai Industara, Computer da sauran kekunan dinki na zamani amma ba irin keke tako-tako ba.
Inda anso a taimaki iyayen mu mata ba injin nika ya kamata a basu ba, a daidai wannan lokacin da rayuwa tayi tsada, akwai masu sana’ar abincin siyarwa da masu awara kamata yayi a samar da kayan abinci, waken suya da man gyada domin saukaka musu rayuwa da ganin cewa sun dogara da kansu.
Amma da yake a wulakance alumma suke a idon wannan wakilin kuma munfi kama da kaskantu ba yaya ba, l a gurin shi. Sai yaga dacewar wofantar da bukatun da suka fi dacewa damu tare da cusa mana abin da yayi daidai da ra’ayin sa don mu dawwama a matsayin yan barandar siyasa masu neman abinci ba ilimi ko arziki ba. Yanzu kwakwalwa da tunani ake ginawa dan Adam a fadin duniya ba gina ciki ko mayar da samari mabarata a kafar sada zumunta ba.
A nawa tunanin bawa iyayen mu mata jarin kayan abincin siyarwa irin su:- Shinkafa da wake, Waken suya, Man gyada da Kiwon kaji zai fi injin markade amfani a gurin su, musamman a wannan yanayin da muke ciki. Bangaren masu dinki kuwa samar da masana’antar dinki da kuma sababbin kekuna na zamani ba tako-tako ba wanda aka daina yayin su a
A karshe ina da tambaya, wane taro wakilinmu ya taba yi na tallafawa dalibai su samu ingantaccen ilimi tunda ya fara wakiltar mu?