Hukumar Kwato Dukiyar Gwamnati Daga Hannun Ma’aikata (ICPC), ta ce ta kwato naira bilyan 16 daga hannun barayin gwamnati a Ma’aikatar Harkokin Noma ta Tarayya, a cikin 2020.
Shugaban ICPC, Bolaji Owasanoye ne ya bayyana haka a wata taron da ake yi ta ‘Zoom’, mai take, “Taron Kasa Kan Yaki Da Wawurar Kudade A Ma’aikatun Gwamnati”.
Owasanoye ya ce an karkatar da kudaden ta hanyoyin da tilas zargin harkalla ya shiga, kamar yadda aka yi hada-hadar ba bisa tsari ba.
ICPC ta ce jami’an ta sun gano an kimshe kudaden a cikin wani boyayyen asusun a CBN, ta yadda ba su yadda za a yi Gwamnati ta iya sanin yadda aka yi da kudin.
Har yau da Owasanoye ya kara da cewa wasu kudaden da su ka gano kuma an damfare su a cikin asusun wasu daidaikun baragurbin mutane. Wasu kuma an rubuta cewa an kashe su kan wasu ayyukan da ko kadan ba su shafi ayyukan gwamnati ba.
“Duk da cewa annobar cutar korona ta kawo tsaiko kan binciken karkatar da kudade da ICPC ta rika yi, an samu karbo kudaden daga CBN, lokacin da Ma’aikatar ta rubuta takarda cewa ta na bukatar kudaden domin a yi amfani da su wajen bai wa marasa galihu tallafi a lokacin korona.
“Har yanzu ICPC ba ta gama bindiggin karkatar da kudaden ba.” Inji shi.
ICPC ta kuma gwno yadda aka biya wasu ‘yan kwangila kudaden ayyukan da ba su yi ba. An kuma biya wasu kudaden ayyukan da su ka yi har biya rubi biyu.
“Wasu kudin ma karkatar da su aka yi a gonakin wasu jami’an Ma’aikatar Gona ta Tarayya.”
“An kuma samu har naira bilyan 2.5 a cikin asusun mamacin da ya karkasa kudaden a asusun sa da na makusantan sa.
Ya ce ICPC ta cika shekaru 20, kuma a cikin shekarun nan ta samu takardun tsegunta masu karkatar da kudade har wasiku 20,000.
“ICPC ta gamsu da sahihancin wasiku 5000, kuma a cikin su an gurfanar da kamar mutum 1000 a kotu.
Discussion about this post