Shugaban Kwamitin binciken tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu, Maishari’a Ayo Salami ya karyata lauyoyin da suka ce ya rika maimaita cewa yana yin dana sanin shugabantar kwamitin da ake binciken Magu.
Idan ba a manta ba wasu lauyoyin Magu biyu sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa a gabansu Salami ya rika yin da-na-sanin shugabantar wannan kwamiti da yake yi.
Lauyoyin masu suna Tosin Ojaoma da Zainab Abiola, duk sun shaida wa PREMIUM TIMES a lokutta daban daban cewa maisharia Salami ya bayyana da bakin sa cewa yayi dana sanin saka kansa a cikin wannan bincike.
” Muna zaune a lokacin da Salami ya zo ya zauna sai ya girgida kai ya ce, na yi nadamar shugabantar wannan kwamiti na binciken Magu.
” Salami ya cire kyallen goge fuska yana ta goge fuskar sa yana cewa, kaico na yi danasanin saka kaina a cikin wannan kwamiti din. Ya rika goge fuskarsa.
” Na tambayeshi cewa me ya sa ya ke cewa haka? Amma bai amsani ba, yana ta maimaita cewa gaskiya yayi da-na-sanin wannan aiki da yake yi.
Lauyan ya ce ko da suka tambayeshi ko don ya ga cewa har yanzu ba a iya samun Magu da aikata laifi ko daya ba. Salami ya cigaba da goge fuskarsa ne kawai yana cewa yayi nadamar shiga cikin wannan kwamiti.
Salami ya ce bai furta wadannan kalamai ba.
Shi dai wannan kwamiti, a asirce a ke zaman sa, babu dan jarida ko daya da aka amince ya shiga dakin da kwamitin ke zama bayan ba haka doka ta ce ba.
Discussion about this post