Babu hannu na a ɓacewar naira bilyan 2.72, Kuɗin ciyar da daliban kwaleji – Minista Sadiya

0

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana cewa babu hannun ta a bacewar wasu daga cikin kudi naira biliyan biyu da miliyan saba’in da biyu (N2.72b) daga asusun shirin ciyar da ‘yan makarantar kwalejojin Gwamnatin Tarayya saboda zaman annobar korona kamar yadda wasu ke yadawa a kafafen watsa labarai.

An riƙa yaɗa labarin ne bayan da shugaban hukumar binciken cin hanci da rashawa (ICPC), Farfesa Bolaji Owasanoye, ya gabatar da wani jawabi a wajen Babban Taron Kasa Kan Raguwar Cin Hanci, karo na 2, wanda aka yi a gaban Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Kasa a Abuja a ranar Litinin.

Rahoton shugaban na ICPC ya fada ƙarara cewa: “binciken farko ya nuna cewa wani bangare na kudi naira biliyan 2.67 an kautar da su zuwa asusun wasu mutane. Kuma (binciken) ya nuna cewar wani babban ma’aikacin Ma’aikatar Aikin Gona (mun boye sunan sa), wanda yanzu ya rasu, shi da wasu aminan sa, sun sace sama da naira biliyan 2.5.”

Mai ba Minista Sadiya shawara kan harkokin watsa labarai, Nneka Ikem Anibeze, ta ce wasu magulmata sun murda bayanin na shugaban ICPC, su ka yi masa muguwar fassarar cewa wai akwai hannun Minista Sadiya a cikin lamarin sace kudin.

Ta ce ministar ta na mai sanar da duniya cewa shirin ciyar da ‘yan makaranta na Gwamnatin Tarayya da ake magana a kan sa ya bambanta da shirin ma’aikatar ta na ciyar da ‘yan makaranta wanda wani sashe ne na shirin ta na inganta rayuwar al’umma.

Kuma ta yi nuni da cewa shirin ciyarwar da ake bincike a kai shi ne wanda ake ciyar da daliban da ke kwalejojin Gwamnatin Tarayya da ke fadin ƙasar nan, kuma ba a karkashin Ma’aikatar Harkojin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ya ke ba, domin ita ta kula ne da shirin ciyar da ‘yan makarantar firamare ‘yan aji 1 zuwa 3 a makarantun gwamnati da ke ƙasar nan.

Ta ƙara da cewa ba ma’aikatar ta ko ita ce ta ke kula da wancan shirin da ake kira “Home Grown School Feeding” ba.

A cewar ta, ko kaɗan kuɗin shirin ba su biyo ta hannun ta ko ta ma’aikatar ta ba.

Ta ƙara da cewa akwai sama da naira biliyan biyu da rabi da ake cewa wani babban ma’aikaci da abokan sa sun zaftare, abin ya faru ne a wata ma’aikatar daban, ba Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ba.

Ta ce dukiya ta kimanin naira biliyan 16 da ICPC ta karbe daga cikin kudin da aka sace din a waccan ma’aikatar, wadanda aka ce an saka su a asusun wasu mutane ba don gudanar da aikin da ya shafi gwamnati ba, ba a Ma’aikatar Harkokin Agaji ba ne.

Ma’aikatar ta ce wadanda su ke zagi ko sukar Sadiya a kan wannan batun, su na dai yi ne saboda tsana da kuma nuna mata rashin adalci.

Ta yi kira ga hukumar ICPC da ta wallafa sunayen dukkan mutane da kwalejojin Gwamnatin Tarayya da shugabannin makarantun da ake zargi da sa hannu cikin wannan almundahana, kuma a rufe asusun bankin su inda su ka boye kuɗin.

Saboda haka ma’aikatar ta na kira ga dukkan jama’a da su yi watsi da wancan rahoton aryar da wasu ke yadawa, domin kuwa ko kadan babu hannun ministar a wannan shirin na ciyar da daliban kwaleji.

Share.

game da Author