Idan ba a manta ba tun bayan ƙirkƙiro da sabbin masarautu a jihar Kano da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje yayi, ya aika da ƙudiri majalisar jihar domin a yi dokar da za a rika yin karba-karba a shugabantar majalisar sarakunan jihar.
Kamar yadda gwamna Ganduje yaso, duk bayan shekara biyu shugabancin majalisar sarakunan jihar zai koma hannu wani sarkin cikin hudun da ya kirkiro.
Tun a wancan lokaci masu fashi baki sun yi ikirarin cewa tabbas gwamnati ta kirkiro da tsarin karba-karba ne domin ta rage wa sarkin Kano Sanusi karfin Iko a majalisar sarakunan jihar.
A ranar Talata majalisar jihar ta bayyana amincewa da kudirin ta zama doka, sai dai ba yadda aka so a lokacin da Sanusi ke kan kujerar sarautar Kano.
Majalisar ta amince da kada ayi karba-karba, sarkin Kano zai cigaba da zama shugaban majalisar sarakunan jihar na dindindin.
Bayan haka majalisar ta kara mutum daya a cikin masu zaben sabon sarki, daga mutum 4 zuwa 4.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Kabiru Dashi ya ce majalisar ta yi hakane domin kada a rika samun rudani a duk lokacin da bukatar zaben sarki ya taso.
Sannan kuma majalisar ta amince a rika zaben sabon sarki cikin kwana uku da cire Sarki ko kuma ya rasu.
Discussion about this post