Ba ruwan Minista Sadiya a satar kudin ciyar da dalibai har naira biliyan 2.7, inji ICPC

0

Hukumar Binciken Ayyukan Cin Hanci Da Rashawa (ICPC) ta bayyana cewa ko kadan ba Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ba ce ta ke nufi da saka hannu cikin sace wasu kudi na shirin ciyar da dalibai a lokacin zaman korona.

Wasu kafafen yada labarai da mutane a soshiyal midiya su ka baza labarin cewa wai ana zargin Minista Sadiya Umar Farouq da taka rawa wajen sace sama da naira biliyan biyu da miliyan dubu sittin da bakwai (N2.67b) daga cikin kudin da aka ware don ciyar da ɗ
dalibai lokacin da ake zaman dirshan saboda annobar korona.

Hakan ya biyo bayan jawabin da shugaban hukumar, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya yi a ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2020 a wajen Babban Taro na Kasa kan Raguwar Cin Hanci da Rashawa, karo na biyu, a Abuja.

Hukumar ICPC ta ce rahotannin sun tafka kuskuren cewa Minista Sadiya ce ta karkatar da kuɗin na shirin da ake kira “Home-Grown School Feeding Programme”. 

Abin da Farfesa Owasanoye ya fada a jawabin sa a taron, shi ne, “… mun gano cewa wasu kudaden da aka biya ga wasu kwalejojin gwamnatin tarayya (makarantun sakandare) don ciyar da dalibai ‘yan sakandare, wanda sun kai N2.67 biliyan lokacin zaman dole a sa’ilin da ‘yan makaranta ba su zuwa makaranta, sun shige aljifan mutane ne.

“Mun soma bincike kan wadannan abubuwan da mu ka gano.”

Hukumar ta ce ta na so ta fadakar da jama’a cewa “ciyarwar ‘yan makaranta” da shugaban ICPC ya ambata ita ce ta dalibai da ke kwana a Kwalejojin Gwamnatin Tarayya, wadanda duk su na zaune a gida a lokacin zaman dole na annobar COVID-19.

Ta ce: “Wannan ba shirin ‘Home-Grown School Feeding Programme’ ba ne wanda Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ke aiwatarwa. 

“Hukumar ta gano a lokacin da ta ke nazari kan takardun Gidan Yanar Budadden Asusu (Open Treasury Portal) cewa kudaden da aka kasafta za a rika kashewa a wata-wata kan ciyar da daliban makarantun sakandare na wasu daga cikin Kwalejojin Gwamnatin Tarayya ana kautar da su zuwa asusun wasu mutane.

“Mun fitar da wannan sanarwar ne domin mu yi karin haske kan bayanin da Shugaba ya yi.

“Saboda haka, mu na sanar da dukkan jama’a cewa su yi watsi da wadancan rahotannin da su ke cewa shirin ciyar da daliban makarantun firamare ne mu ka yi magana a kai.”

Hukumar ta fada wa duk mai bukata cewa zai iya sauko da cikakken jawabin da shugaban ya yi daga gidan yanar hukumar da ke intanet a wannan adireshin, wato www.icpc.gov.ng.

Share.

game da Author