Ni dai a mahangata ba wai rashin tsaro bane babbar matsalar Najeriya rashin aikin yi shine kusan ummul aba’isin rashin tsaro a yau, domin kuwa a yadda matsalar da faro tun daga farko shine, dubban mutane da suke rasa gidajensu da dukiyoyinsu sukan rasa samun mafitar rayuwa ta ko wacce irin fuska, sukan wayi gari babu cin yau babu na gobe.
Talaka masu iyalai daga cikinsu sukan koma yin bara akan titi wasu daga cikinsu Kuma ƴaƴansu mata su koma yin karuwanci domin neman abincin bakinsu saboda basa samun wani tallafi daga hanun gwamnati wanda a dalilin hakan sukan iya aikata komai idan ka musu tayi indai zaka biyasu to za su yi shi ko menene.
A yau an wayi gari dayawa daga cikin mutane ‘yan kungiyar boko haram da sauran dukkanin kungiyoyin ta’addaci wasu sukan fara ne da shaye shaye su koma sace sace har su kai ixuwa fashi da makami da ta’addacinci duk ta dalilin rashin aikin da zasuyi domin su iya rike kansu tare da iyalansu, saboda dayawa daga cikinsu da zaran an kamasu zaka gansu duk talakawa ne yunwa ta gama cin jikinsu, saboda rana tsaka za’azo ayi maka tayin milyoyin kudade a saka aiki ta yadda wadannan kudaden zasu gusar da tunaninka har sai ka aikata kazo kana nadama, shiyasa dayawa daga cikin yan kungiyar boko haram da zaran an kamasu suke nadama wasu kuma da kansu ma suke ajiye makamansu.
A wani binciken dana gudanar na gano cewa a Najeriya munada Jami’o’i mallakin gwamnatin tarayya, na jihohi da da masu zaman kansu har guda dari da hamsin da uku (153). Kuma a duk shekara ko wacce daga cikinsu tana yaye dalibai sama da guda dari uku a duk shekara (300). Idan ka lissafa zaka samu 300 × 153 = 45,900 ( Mutum dubu arba’in da biyar da dari tara a duk sheka)
Kwalejojin ilmi mallakin gwamnatin Tarayya da masu zaman kansu, har dari da hamsin da biyu (152). Suma aduk shekara ko wacce daga cikinsu a akalla yaye dalibai guda (200). Idan ka lissafa zaka samu 200 × 152 = 3,400 (Mutum dubu uku da dari biyar aduk shekara)
Kwalejojin Kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin Tarayya da na Jihohi(112). Suma Kuma aduk shekara ko wacce daga cikinsu tana yaye dalibai akalla guda (350) idan ka lissafa zaka samu 350×112 = (39200). (Mutum dubu talatin da tara da dari biyu aduk shekara)
Kwalejojin koyan ayyukan Noma kimanin guda 77 suma aduk shekara daga ko wace makaranta ana samun yayayyin dalibai guda (150) daga ko wace makaranta Idan ka lissafa zaka samu 150 × 77 = 11,550 ( Mutum dubu sha daya da dari biyar da hamsin da biyar aduk shekara)
Kwalejojin Koyan aikin Asibiti Kimanin guda (101) kuma suma ko wace makaranta daga cikinsu tana yaye a dalibai akalla guda 100 aduk shekara. Idan ka lissafa zaka samu 101 × 100 = 10,100 ( Mutum dubu goma da dari daya aduk shekara).
Idan ka hada gaba daya ka lissafa iya wadannan zaka samu aduk shekara ana yaye dalibai kimanin guda dubu dari da goma da dari daya da hamsin (110,150).
Amma acikinsu 4/10 ne suke samun aikinyi, Sauran duk suna zaman jira kuma still ‘yan next year suzo su karu a kansu.
A hakan kuma akwia ‘yan secondary wadanda da basuci gaba da karatu ba suma sunanan babu madafa.
A halin da ake ciki yanzu haka a wasu daga cikin jahohi akalla yakai kimanin shekara sbiyar (5) ba tare da an dauki aiki ba ta ko wani fanni idan kuwa hakane graduate marasa aiki kake tsammani samu acikin wadannan jajohin ?
A wata sanarwa da kasa ta fitar a 2019 shine out of 100% people in Nigeria 55.4 percent a unemployed only 44.6 percent are employe
Kunga kenan wadanda basu da graduate din da basu da aiki sunfi masu aiki yawa a kasa.
-Shin ko gomnati tasan cewa dayawa daga cikin wadannan marasa aikinyi iyayensu sun hana kansu jindadin rayuwa sun turosu karatu tare da sa ran idan sun gama suka samu abinyi zasu taimaki kansu kuma su taimaki iyaye nasu?
-Wani iyayensa noma sukeyi su biya masa kudin makaranta
-Wata mahaifiyarsa ne take ‘yan sana’oi ta biya masa kudin makaranta
-Wani shine yake biyawa kansa
-Wani ‘yan uwa ne da abokan arziki suke biya masa.
Amma saika gama karatun kazo ka rasa aikinyi.
A yau an wayi gari kusan ko wacce jaha a arewacin Nigeria tana fama da. ‘ta’addanci garkuwa da mutane, fashi, sata. Da sauransu
Wanda duk idan mukayi tunanin zamuga kusan duk wanda sukeyi sunayi me don neman kudi wanda idan da suna da abinyi to da ba lallai ne su aikata ba….
Saboda haka ina kira ga shugabanni tun daga kan mai girma shugaban kasa har zuwa kan duk wani Wanda zai iya bada tasa gudumawar wajen samar da aikinyi a al’umma to su duba wannan shawarar dana bayar tayiwu ubangiji ya dubemu ya kawo mana mafita…
Amma magana ta gaskiya shine a fara magance rashin aikinyi to Insha Allah tsaro zai samu…
Ya Allah ka kawo mana dauki, ka ka kawo mana mafita. Amen
Daga, Comr Bashir Suleiman